AQIIDAR SHEIK BIN BAZ DA SAURAN AHLUS SUNNAH WAL JAMA’AH GAME DA RUQYAH DA YIWUWAR YIN MAGANA DA ALJANI TA HARSHEN WANI MUTUM(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)


Wani dan’uwa ya tambaye mu
cewa: Ko mene ne aqiidar marigayi
Sheik Abdulaziz Bin Baz shugaban
majalisar malamai ta Saudiyya
game da Ruqyah da kuma yiwuwar
a yi magana da aljani ta harshen
mutum? Mutumin ya ce ya yi
wannan tambayar ce saboda ya ji
wasu malaman na cewa hakan
kfirci ne kuma bokanci ne!
AMSA:
Gaskiya ne Muutazilaawa da Shi’ah
Raafidhah da ‘Yan dogara da
hankali sun tafi a kan cewa ba zai
yiwu ba sam a ce aljani na iya
shiga cikin jikin mutum, ballantana
ma a ce wai wani mutum zai iya
yin magana da aljanin ta harshen
wanda aljanin ya shige shi, su
wadannan kungiyoyin bidi’ah suna
ganin masu yarda da hakan a
matsayin wasu bokaye ko ma wasu
kafirai. Amma su Ahlus Sunnah
Wal Jama’ah, saboda dogara da
Alkur’ani da Sunnah da suke yi, su
sun yi imani da cewa: aljani na iya
shiga cikin jikin mutum saboda ya
cutar da shi, haka nan kuma sun
yarda da cewa: mutum na iya
magana da aljani ta harshen
wanda aljanin ya shige shi.
************************
Lalle da yake shi Sheik Abdul-Azizi
Bin Abdillah Bin Baz yana daga
cikin shugabannin Ahlus Sunnah
Wal Jama’ah na Duniya to wannan
shi ne aqiidarsa shi ma, ga ma
abin da yake cewa cikin littafinsa
mai suna: Iidhaahul Haqqi Fii
Dukhuulil Jinniyyi Fil Insiyyi shafi
na 6-7:-
{ ﺗﻠﺒﺲ ﺍﻟﺠﻦ ﺑﺒﻌﺾ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺎﺕ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﻳﺎﺽ ﻓﻘﺮﺍ
ﻋﻠﻴﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺸﺎﻳﺦ ﻭﺫﻛﺮ ﺍﻟﺠﻨﻲ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﻭﻋﻈﻪ
ﻭﺍﺧﺒﺮﻩ ﺑﺎﻥ ﺍﻟﻈﻠﻢ ﺣﺮﺍﻡ ﻭﻛﺒﻴﺮﺓ ﻋﻈﻴﻤﺔ، ﻭﺩﻋﺎﻩ
ﺍﻟﻰ ﺍﻻﺳﻼﻡ ﻓﺎﺳﻠﻢ، ﺛﻢ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﻋﻨﺪﻱ ﺑﺎﻟﻤﺮﺍﺓ
ﻓﺴﺎﻟﺘﻪ ﻋﻦ ﺍﺳﺒﺎﺏ ﺩﺧﻮﻟﻪ ﻓﻴﻬﺎ ﻓﺎﺧﺒﺮﻧﻲ
ﺑﺎﻻﺳﺒﺎﺏ ﻭﻧﻄﻖ ﺑﻠﺴﺎﻥ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﻟﻜﻨﻪ ﻛﻼﻡ ﺭﺟﻞ
ﻭﻟﻴﺲ ﻛﻼﻡ ﺍﻣﺮﺍﺓ، ﻭﻫﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﺮﺳﻲ ﺍﻟﺬﻱ
ﺑﺠﻮﺍﺭﻱ ﻭﺍﺧﻮﻫﺎ ﻭﺍﺧﺘﻬﺎ ﻭﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺸﺎﻳﺦ
ﻳﺸﻬﺪﻭﻥ ﺫﻟﻚ ﻭﻳﺴﻤﻌﻮﻥ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﺠﻨﻲ ﻭﻗﺪ ﺍﻋﻠﻦ
ﺍﺳﻼﻣﻪ ﺻﺮﻳﺤﺎ، ﻓﻨﺼﺤﺘﻪ ﻭﺍﻭﺻﻴﺘﻪ ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ
ﺍﻥ ﻳﺨﺮﺝ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﻭﻳﺒﺘﻌﺪ ﻋﻦ ﻇﻠﻤﻬﺎ
ﻓﺎﺟﺎﺑﻨﻲ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻗﺎﻝ : ﺍﻧﺎ ﻣﻘﺘﻨﻊ ﺑﺎﻻﺳﻼﻡ،
ﻭﻏﺎﺩﺭ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﺍﻟﻤﺬﻛﻮﺭﺓ ﺑﻠﺴﺎﻧﻬﺎ ﺍﻟﻤﻌﺘﺎﺩ
ﻭﺷﻌﺮﺕ ﺑﺴﻼﻣﺘﻬﺎ ﻭﺭﺍﺣﺘﻬﺎ ﻣﻦ ﺗﻌﺒﻪ، ﺛﻢ ﻋﺎﺩﺕ
ﺍﻟﻲ ﺑﻌﺪ ﺷﻬﺮ ﻭﺍﺧﺒﺮﺗﻨﻲ ﺑﺎﻧﻬﺎ ﺑﺨﻴﺮ ﻭﻋﺎﻓﻴﺔ .{
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Aljani ya cakuda da
sashin wasu mata musulmi a
Riyadh sai sashin malamai ya yi
masa karatu, ya tunatar da aljanin
girman Allah, ya yi masa wa’azi, ya
ba shi labarin cewa zalunci
haramun ne kuma zunubi ne mai
girma, kuma ya kira shi zuwa ga
Musulunci ya musulunta, sannan
sai suka zo wajena tare da matar
na tambaye shi dalilan shigarsa
cikinta, ya gaya mini dalilan, ya yi
magana a bisa harshen matar sai
dai maganar namiji ne ba maganar
mace ba, ita kuwa tana zaune cikin
kujera a kusa da ni, dan’uwanta da
‘yar’uwarta da sashin wasu
maluma suna shaidar haka suna
kuma jin maganar aljanin, alhalin
ya bayyanar da shiga
musuluncinsa a fili, sai na yi masa
nasiha, na yi masa wasiyyar ya ji
tsoron Allah ya fita daga wannan
matar, ya nisanci zaluntar ta, sai ya
amsa mini zuwa ga hakan ya ce:
Ni na gamsu da Musulunci, ya bar
matar da aka ambata ta harshenta
wanda aka sani, ta kuma fahimci
lafiyarta da samun hutunta daga
gajiyar da ya sa mata, sannan ta
dawo wurina bayan wata guda ta
gaya mini cewa tana cikin alheri
da lafiya)).
Muna rokon Allah Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah,
Ya raba mu da fadawa cikin sharrin
yan bidi’ah. Ameen.

Advertisements

2 thoughts on “AQIIDAR SHEIK BIN BAZ DA SAURAN AHLUS SUNNAH WAL JAMA’AH GAME DA RUQYAH DA YIWUWAR YIN MAGANA DA ALJANI TA HARSHEN WANI MUTUM(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

  1. Allah yasaka da alkhairi. Bayan haka inaso ayiminba bayanin yadda ake ruqya sunnance dakuma ayoyi ko addua da akeyi

  2. assalamu alaikum malam game da shigar aljani jikin mutum wannan babu matsala cikinsa domin hadisi ingantatce yayi nuni akan haka.matsalar kawai yadda ake fitar da shi aljanin har ma yayi magana shin MANZON ALLAH YAYI HAKA KAMAR YADDA MASU YIN RUQIYYAR SUKE YI A YAU???!

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s