HALACCIN SANYA ZOBE A HANNUN DAMA KO A HANNUN HAGU(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)


Ya halatta Musulmi ya sanya zobe
ko dai a yatsar hannunsa na dama
ko kuwa a yatsar hannunsa na
hagu, saboda wadannan dalilai:-
1. Imamu Muslim ya ruwaito
hadithi na 2094 daga Sahabi Anas
Dan Malik cewa:-
(( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﺒﺲ
ﺧﺎﺗﻢ ﻓﻀﺔ ﻓﻲ ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻓﻴﻪ ﻓﺺ ﺣﺒﺸﻲ ﻛﺎﻥ
ﻳﺠﻌﻞ ﻓﺼﻪ ﻣﻤﺎ ﻳﻠﻲ ﻛﻔﻪ )).
Ma’ana: ((Lalle Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya sanya
zoben azurfa a damarsa cikinsa
akwai mahadar zobe na irin na
habasha, ya kasance ya kan sanya
mahadar zoben ta bangaren tafin
hannunsa)).
2. Imamu Muslim har yanzu ya
ruwaito hadithi na 2095 daga
Sahabi Anas Dan Malik cewa ya
ce:-
(( ﻛﺎﻥ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ
ﻫﺬﻩ، ﻭﺃﺷﺎﺭ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻨﺼﺮ ﻣﻦ ﻳﺪﻩ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ )).
Na’ana: ((Zoben Annabi mai tsira
da amincin Allah ya kasance ne
cikin wannan, sai ya yi ishara zuwa
ga karamar yatsa daga hannunsa
na hagu)).
3. Imamu Abu Dawud ya ruwaito
hadithi na 4229 daga Ibnu Ishaqa
ya ce:-
(( ﺭﺃﻳﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻠﺖ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﺎﺗﻤﺎ ﻓﻲ
ﺧﻨﺼﺮﻩ ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻓﻘﻠﺖ : ﻣﺎ ﻫﺬﺍ؟ ﻗﺎﻝ : ﺭﺃﻳﺖ ﺍﺑﻦ
ﻋﺒﺎﺱ ﻳﻠﺒﺲ ﺧﺎﺗﻤﻪ ﻫﻜﺬﺍ ﻭﺟﻌﻞ ﻓﺼﻪ ﻋﻠﻰ
ﻇﻬﺮﻫﺎ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻻ ﻳﺨﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺍﻻ ﻛﺎﻥ ﻳﺬﻛﺮ
ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻳﻠﺒﺲ
ﺧﺎﺗﻤﻪ ﻛﺬﻟﻚ )).
Ma’ana: ((Na ga wani zobe tare
Salt Dan Abdullah cikin karamar
yatsarsa ta hannun dama, sai na
ce: Mene ne wannan? Sai ya ce:
Na ga Dan Abbas ya kan sanya
zobensa kamar haka ya sanya
mahadar zoben nasa ta bayan
tafinsa. Ya ce: Ba a tsammanin
Ibnu Abbas face ya kasance yana
ambaton cewa lalle Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah haka ya
kasance yake sanya zobensa)).
Wannan Hadithi Albani ya inganta
shi.
4. Ya zo cikin littafin Aljaami’us
Sagir Wa Ziyaadatihi, Hadithi na
4899 kamar haka:-
(( ﻛﺎﻥ ﻳﺘﺨﺘﻢ ﻓﻲ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).
Ma’ana: ((“Annabi” Ya kasance
yana sanya zobe a hagunsa)).
Albani ya inganta shi.
5. Har yanzu ya zo cikin Littafin
Aljaami’us Sagir Wa Ziyaadatihi,
Hadithi na 4900 kamar haka:-
(( ﻛﺎﻥ ﻳﺘﺨﺘﻢ ﻓﻲ ﻳﻤﻴﻨﻪ )).
Ma’ana: ((“Annabi” Ya kasance
yana sanya zobe ta damarsa)).
Albani ya inganta shi.
******************************
TA INA AKE SANYA “Fassin zobe”?
WATAU MAHADAR ZOBEN WANDA
YAWANCI AKE MASA ADO NA
MUSAMMAN?
Amsa: Kana iya sanya shi ta
bangaren cikin tafin hannu, haka
nan kana iya sanya shi ta
bangaren bayan tafin hannu;
saboda Hadithan da muka ambata
a sama.
***************************
A WACE YATSA CE YA KAMATA
NAMIJI KO MACE SU SANYA
ZOBEN NASU?
Amsa: Imamun Nawawi ya ce cikin
littafinsa “Sharhun Nawawi Alaa
Sahihi Muslim”7/188 kamar haka:-
(( ﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺟﻌﻞ ﺧﺎﺗﻢ
ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻨﺼﺮ، ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺗﺘﺨﺬ
ﺧﻮﺍﺗﻴﻢ ﻓﻲ ﺃﺻﺎﺑﻊ )).
Ma’ana: ((Musulmi sun yi Ijmaa’i a
kan cewa Sunnah ita ce namiji ya
sanya zobe a karamar yatsa, amma
ita mace tana iya sanya zobba
cikin yatsu dayawa)).
*************************************
SHIN ZOBEN AZURFA NE KAWAI
YAKE HALATTA?
Amsa: Zoben zinare da azurfa da
ma ko mene ne yana halatta ga
Mata.
Sannan zance mafi inganci shi ne:
Ko wane zobe yana halatta ga
Maza ma amma banda zoben
zinare.
Yana daga cikin hujjar wannan
magana tamu abin da Imamun
Nawawi ya ce cikin littafinsa
“Sharhun Nawawi Alaa Sahihi
Musulim”7/177 :-
(( ﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺎﺣﺔ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﺬﻫﺐ
ﻟﻠﻨﺴﺎﺀ، ﻭﺃﺟﻤﻌﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺗﺤﺮﻳﻤﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ )).
Ma’ana: ((Musulmi sun Ijmaa’i a
kan halaccin zoben zinare ga Mata,
sannan sun yi Ijmaa’i a kan
haramcinsa a kan Maza)).
Akwai wasu hujjojin daban banda
wannan. Muna rokon Allah Ya
taimake mu, Ya karfafa Addininmu,
Ya kare mana Al’ummarmu.
Ameen.

Advertisements

One thought on “HALACCIN SANYA ZOBE A HANNUN DAMA KO A HANNUN HAGU(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s