RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 02(Dr. Mansur Sokoto)


Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
BABI NA DAYA
1.0 Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama Kafin watan Azumin
Ramalana:
Wannan babi zai yi tsokaci ne a kan
yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ke kasancewa kafin watan
Azumin Ramalana ya kama, ta hanyar
yawaita Azumin nafila da yake yi a
cikin watan Sha’abana, da yi wa
Sahabbansa bushara da kamawar
watan, tare da yi masu bayanin
abubuwan da yake dauke da su na
falala, da wasu abubuwa masu kama
da haka.
1.1 SHIMFIDA:
Kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama mutum mai matuqar tsoron
Allah Subhanahu Wa Ta’ala da gudun
duniya, da tsananin kwadayin abin da
Allah Ta’ala ya yi tanadi na
kyakkyawan sakamako gobe qiyama.
Sai hakan ta sa yake qara murna da
farin ciki, a duk lokacin da wani
yanayi na saukar alherin Allah da
rahamarsa da jinqayinsa ke qara
qamari. Yana kuwa yin haka ne
Sallallahu Alaihi Wasallama saboda
cika umurnin Allah Subhanahu Wa
Ta’ala da yake cewa: “Kace, su yi farin
ciki da samun falalar Allah da
rahamarsa. Wannan shi ne mafi alheri
fiye da abin da suke Tarawa.” (10:58)
Wannan aya na tabbatar da cewa yin
farin ciki da abin da Allah Ta’ala ya
saukar a cikin Alqur’ani, ya kuma hori
bayinsa da aikatawa, wanda ya hada
da abubuwa na wajibi da na
mustahabbi, kamar Azumin Ramalana,
wanda kusan babu wani wajibi da ya
sha gabansa. To, yin farin ciki da
samuwar wadannan abubuwa a
falsafar Musulunci, shi ne mafi zama
alheri, bisa ga duk wani farin ciki da
bawa zai yi a kan tarin tulin wani abu
na duniya.
Malam Sa’adi na cewa, qarin bayani a
kan wannan aya: “Ko alama, ba a hada
ni’imar addini da ta abin duniya;
matsayinsu ba daya ba. Ni’imar addini
ta hada arzikin duniya ne, da na lahira
baki daya. A yayin da shi kuwa abin
duniya, ko a duniyar ba ya da wani
garanti. Domin kuwa gishirin qoqo ne,
ana cikin kadi yake qarewa. Saboda
haka ne Allah Ta’ala ya hori musulmi
da yin farin ciki a kan samuwar falala
da rahamarsa na addini. Domin hakan
na lamunce masu kwanciyar hankali
da nishadi da godiya ga Allah Ta’ala.
Wanda a sakamakon haka sai su qara
samun qwarin guiwa, da tsananin
kwadayi da sha’awar ilmi da inganta
imaninsu. Wannan shi ne farin ciki na
Shari’a. Ita kuwa murna a kan wani
abu na sha’awoyin duniya da jin
dadinta, ko natsuwa da faruwar wata
masha’a, aikin banza ne. Domin kuwa
Allah Ta’ala ya yi tir da masu yin
annashawa don abin duniya. Kamar
yadda yake ba mu labarin irin yadda ta
kasance tsakanin Qaruna da
mutanensa, inda suka ce masa; “Kada
ka yi fahariya, lalle ne Allah ba ya son
masu fahariya (da abin duniya)
.” (28:76).
Haka kuma Allah Subhanahu Wa
Ta’ala ya yi wa wasu mutane kashedi
da yin bugun gaba saboda wani abu
da suka mallaka na barna, sabanin
abin da Manzanni suka zo da shi na
shiriya, inda yake cewa: “Sa’annan a
lokacin da Manzanninsu suka je masu
da hujjoji bayyanannu, suka yi farin
ciki da abin da ke wurinsu na
ilmi.” (40:83) wannan kenan. Sannan
kuma tabbataccen abu ne cewa, babu
wani abu da ke gaggauta kusanta
bawa da Ubangijinsa, da daukaka
alqadarinsa tare da lamunce masa
yardar Mahalicci, da saka shi gaban
sahu, kamar irin watan Azumin
Ramalana da ire-irensa. Matuqar bawa
ya gudanar da ibadodi a cikin irin
wadannan lokutta kamar yadda aka
umurce shi, ta hanyar zare damtse da
yin da’a ga ubangijinsa, lalle ya
rabauta. Saboda haka ne Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya sake
da irin wadannan lokuta. Da zarar an
ce watan Azumin Ramalana ya gabato,
to, sai Ma’aiki ya sha damara ya
shirya ransa da zuciyarsa da gangar
jikinsa, ta yadda zai fuskanci wannan
ibada cikin cikakken nishadi. Wanda
hakan za ta ba shi damar cin moriyar
watan baki daya.
Muhimman hanyoyin da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ke taron
Watan Azumi da su, sun hada da:
A dakace mu a darasi na gaba in Allah
ya so.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s