RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 04( Dr. Mansur Sokoto)


Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
1.5 TABBATAR DA KAMAWAR WATAN
RAMALANA:
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba
yakan soma Azumin Ramalana ba, face
ya tabbatar da kamawar watan, ta
hanyar samun shedar wani mutum
daya da ya ga watan da qwayar
idonsa, ko tabbatar da watan
Sha’abana ya cika kwana talatin.
Wadannan hanyoyi biyu na tabbatar da
kamawar Watan Azumi, na daga cikin
martabobin da wannan addini ya
kebanta da su, kuma wadanda suka
lamunce ma sa dacewa da kowane
zamani da kowane wuri, saboda komai
nasa a fili yake, ta yadda gaba dayan
mutane na iya zama sheda a kai.
Daga cikin Hadissan da ke tabbatar da
dogarar da Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ke yi a kan tabbatar
tsayuwar watan Azumi, a kan ganin
qwayar ido akwai:
→ Hadisin dan Umar Raliyallahu Anhu
wanda ya ce: “Mutane sun sa ido ga
neman ganin jinjirin watan Azumi, sai
na gaya wa Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama cewa tabbas ni na
gane shi. Sai kuwa ya kama Azumi, ya
kuma umurci mutane da su kama.”
→ Sai kuma Hadisin dan Abbas
Raliyallahu Anhuma wanda ya ce:
“Wani Balaraben qauye ya zo wurin
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya
ce: “Tabbas ni na ga jinjirin watan
Azumi.” Sai Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce masa: “Ko ka yi
imani da babu abin bauta wa da
gaskiya sai Allah? ” Shi kuwa ya karba
masa da cewa: “Eh, na yi.” Sai kuma
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya
sake tambayarsa: “Ko ka yi imani da
cewa, Muhammadu Manzon Allah ne?
Balaraben ya ce: “Eh, na yi.” Daga nan
sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
ya ce wa Bilalu: “Tafi ka shelanta wa
mutane kowa ya ta shi da Azumi
gobe.”
Ka ga a cikin wadannan Hadissai,
musamman ma na biyun, akwai
babban darasi, da ke tabbatar da
girman wannan addini. Wanda kuma
ya kamata a ce Malamai da
shugabannin wannan al’umma sun
kwaikwaya. Wato su fahimci cewa
kowane mutum amintacce ne kuma
karbabbe a idon Shari’a, a mataki na
farko. Ba kuma za a qi karbar
maganarsa ba a kan komai, sai idan
wani mugun hali ya bayyana gare shi,
wanda zai soki lamiri da adalcinsa. Ko
kuma a wayi gari tare da fahimtar
cewa, yana da qarancin hankali, ko
kuma ba ya son kowa da alheri sai
kansa.
Wannan ko shakka babu haka yake.
Domin ka ga Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yarda da maganar
Balaraben qauye a kan wani babban
al’amari a Musulunci, wato Azumi, ba
kuma tare da wani irinsa ya goya
masa baya ba, shi Balaraben. Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi
la’akari da kasancewar Azumin
Ramalana ginshiqin addini ba, balle ya
nemi shedar taron jama’a a kan
tsayuwar watansa. Wannan aqida
kuwa, ita ce abin da ya kamta masu
tsananta wa mutane al’murran addini,
su fahimta su kuma kama, tare da
komowa a kan tafarki madaidaici.
→Haka kuma daga cikin Hadissan da
ke tabbatar da dogarar da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi a
kan cikar watan Sha’abana kwana
talatin, kafin ya kama Azumi, idan
ganin watan Azumi da qwayar ido ya
faskara, akwai cewar da ya yi wa
Sahabbai, su dogara a kan ganin
qwayar ido ga watan ba hisabi ba.
Kuma su tabbatar da qarewarsa ta
wannan hanya. Ya ce: “Kada ku kama
Azumi sai an ga wata da qwayar ido.
Haka kuma kada ku aje shi, sai an ga
watan Sallah da qwayar ido. Kuma
kada ku yarda da wata hanya da ba
wannan ba. Idan Kuma kuka kasa
ganinsa saboda wani dalili, to ku bari
sai watan Sha’abana ya cika kwana
talatin. Da zarar mutum biyu sun bayar
da sheda, to ku kama Azumi, ku kuma
aje idan irinsu suka bayar da shedar
qarewarsa.”
→A wani Hadisin kuma da Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Wata kan yi
kwana ashirin da tara. Kada ku kama
Azumi har sai kun ga wata da qwayar
idonku. Idan kuma kuka kasa ganinsa
saboda wani dalili, to ku bari sai
Sha’abana ya cika kwana talatin.”
Saboda haka babu wani dalili da zai
sa mutum ya dauki Azumi kafin a
tabbatar da tsayuwar wata, wai don ko
aka yi. Domin kuwa Shari’a ta riga ta
yi wa al’amarin makama. Saboda haka
ne ma Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi mana kashedi da “Ko-
aka yi” ya ce: “Kada ku kuskura ku
kama Azumi tun watan Ramalana bai
tsaya ba, ku bari sai an gan shi da
qwayar ido, sannan, idan kuma an ga
Sha’abana ta wannan hanya, ku aje.
Idan kuma giragizai suka hana ku
ganin sa, to, ku jira Sha’abana ya cika
qwana talatin.
→ A wani Hadisi kuma ya ce: “Kada
ku yi Azumin nafila da kwana daya ko
biyu kafin watan Ramalana ya tsaya,
sai fa wanda ke yin wani Azumi daban,
shi kam irin wannan mutum ya samu
ya yi Azuminsa.”
Ka ga a shar’ance abin da wadansu
mutane ke yi wato Azumin “Ko-aka yi”
laifi ne. Saboda wadannan Hadissai
da suka tabbatar da rashin halaccin
fara Azumin Ramalana ba tare da an
ga jinjirin watansa da qwayar ido, ko
aka tabbatar da cikar Sha’abana
kwana talatin ba, Ammaru dan Yasir
Raliyallahu Anhu ya ce: “Duk wanda
ya yi Azumin “Ko-aka yi” haqiqa ya
saba wa Baban Qasimu Sallallahu
Alaihi Wasallama.
Amma kuma duk da haka, idan mutum
bai san yadda ake kirdadon tabbatar
da tsayuwar jinjirin wata ba, kuma ba
ya da wanda zai isar masa a kan haka.
Idan ya yi wannan Azumi na “ko-aka
yi” amma da niyyar idan an yin, to, ya
riga ya kimtsa. Idan kuma ba a yin ba,
to, ya dauki Azumin nasa a matsayin
nafila. To, Azuminsa ya inganta a
zance mafi rinjaye. Saboda niyya na
tabbata ne a lokacin da masaniya ta
tabbata, kuma hukuncinsu daya ne.
Idan har ya tabbata cewa watan na
Ramalana ya tsaya, to wajibi ne ya yi
wa Azumin nasa matsaya. Da kuma a
irin wannan hali zai yanke niyyar yin
Azumin nafila ne, ko Azumi kawai, to,
da sakal. Domin kuwa umurnin da
Allah ya yi masa shi ne na daura
niyyar yin Azumin Ramalana, wanda ya
wajaba a kansa, wanda kuma idan ba
shi ya yi ba, da sauran magana.
Amma idan ba ya da masaniya da
cewa watan Azumi ya tsaya, to, ba
wajibi ne a kansa ya yanke wa Azumin
nasa hukunci ba. Duk kuwa Malamin
da ya wajabta yanke hukuncin a irin
wannan hali, to kamar ya daura aure
ne tsakanin ruwa da wuta. Allah shi
ne masani.
Yau da musulmi za su dawo su
qanqame wannan Sunnah ta Manzo.
Su tsaya a kan ganin qwayar ido ko
cikar watan Sha’abana kwana talatin,
don tabbatar da kamawar watan
Azumi, da an huta. Wata fitina ba za ta
sake tashi ba, balle a yi ta jayayya a
kan halaccin yiwuwar amfani da hisabi
da ilimin zamani, ko rashin haka.
Domin kuwa a shar’ance ba ya hallata
a qetare abin da nassi ya zo da shi.
To, kuma ga shi abin da nassi ya
qunsa a wannan al’amari, shi ne
dogara a kan gani na qwayar ido, ba
hisabi ba. Amma kuma duk da haka,
da za a yi amfani da na’aurorin
zamani a tabbatar da haihuwar watan,
sannan ya bayyana a fili a gan shi da
ido, to, wajibi ne a yi aiki da hakan.
Domin kuwa waccan magana ta
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba
ta batse hakan ba, balle. Don cewa ya
yi “Kada ku dauki Azumi ko ku aje shi
sai an ga jinjirin watansa da qwayar
ido.” Idan kuma hakan ta faskara, sai
batun jiran kwanakin Sha’abana su
ciki talatin, kamar yadda nassin ya
tabbatar.
Kuma duk da haka, ba laifi ba ne a yi
amfani da tabaran hangen nesa kamar
kuma yadda yin hakan ba tilas ba ne.
Saboda abin da Sunnah ta nuna
qarara, shi ne dogara a kan gani irin
na qwayar ido, kuma na al’ada kawai.
Kuma shi ne kawai abin da ke wajaba
a kan al’umma don tabbatar da
bayyanar jinjirin wata. Allah shi ne
mafi sani.
Ita kuwa cewar da Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi: “Azumi da idin
qaramar Sallah da layya na karba
sunansu ne idan an yi su tare da
mutane.” Wannan magana na nufin ne
ba ya halatta ga wasu mutane su yi
tunga, su yi Azumi ko Idi ko layya ba
tare da sauran jama’a ba. Lalle ne
kowane musulmi ya yi wadannan
ibadodi tare da Sarki da sauran
jama’a.
Ka ga da Allah zai sa masu wa’azi a
wannan zamani namu su rungumi
wannan aqida, su kuma yayata ta
tsakanin musulmi, da kansu ya hadu a
cikin gunadar da wannan ibada. Kuma
rikitta da rigingimun da ke qamari a
tsakanin tsirarun musulmi a qasashen
gabasci da yammacin Turai sun fada.
Mafi sauqin hanyar da wannan manufa
ke iya tabbata kuwa a hasashena, ita
ce kafa wata hukuma ko cibiya mai
zaman kanta wadda za ta kula da
farawa da qarewar kowane wata kamar
yadda Shari’a ta tanada. Ta haka da
zarar sun tabbatar da tsayuwar watan
Azumi ko qarewarsa, sai su kama
Azumi tare su aje tare. Idan kuwa
suka neme shi qaura-wambai, amma
ganinsa ya faskara, to sai a jira
Sha’abana ya cika kwana talatin,
sannan a dauki Azumin. Shi kuma
Ramalana ya cika talatin din sannan a
aje. Idan kuwa har hakan ta faskara,
wato suka kasa ganin watan a garin
da suke, to sai su yi aiki da ganin da
wani gari na musulmi da ke kusa da
su, suka yi masa. Su dauki Azumi tare
da su. Iyakar abin da za su iya yi
kenan, Allah kuwa ba ya dora wa
rayuwa abin da ba ta iya dauka.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s