RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 09( Dr. Mansur Sokoto)


Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
Ci gaban darasinmu na RAYUWAR
ANANBI SALLALLAHU ALAIHI
WASALLAMA TSAKANINSA DA
UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN
RAMALANA (5)
viii- Aje Azumi:
Ya tabbata cewa Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama ba ya aje Azumi sai
ya tabbatar an ga wata, ko sun cika
kwanaki talatin cur suna Azumin. Dalili
kuwa shi ne, an riwaito yana cewa:
“Kada ku dauki Azumi ko aje shi sai
an ga wata, ku kiyaye wannan. Idan
kuma watan ya shige hazo, to, ku cika
talatin. Idan kuwa shedu biyu suka
sheda, to ku yi Azumi ku kuma aje.”
Kamar mas’alar farko ta kamawar
watan na Azumi, a wannan ma, wato
qarewarsa, muna kira ga mutane da
cewa, zance mafi rinjaye shi ne
dogara a kan ganin wata da qwayar
ido kafin a aje Azumi, ba lissafi irin na
masana taurari ba. Hadisin da muka
kawo a kan wannan magana kuma shi
ne dalili. Amma kuma duk da haka ya
zama wajibi a kan kowane musulmi, ya
yi matuqar qoqarin ganin kan musulmi
ya hadu, ta hanyar gudanar da da
wannan ibada tare da juna.
Babu kuma yadda za a yi wannan
manufa ta tabbata sai kowannen mu
ya kasance mai son gaskiya da karbar
ta, tare da qoqari a kan haduwar kan
al’umma, ta hanyar rashin yin
qememe a cikin al’amarin da ke karbar
ijtihadi, da qyamar son galaba da
rinjaye don wani qabilanci ko son
girma. Dole ne sai mun yaqi
wadannan halaye da dabi’u duk kuwa
da yake Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya
halicce mu da su. Muna roqon Allah
ya shiryar da mu, ya kuma yi mana
jagora. Amin.
Bayan wannan kuma yana da kyau
musulmi mu sani, tattare da
kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama mai matuqar son aikata
nafiloli da mustahabbai, to kwadayinsa
a kan tsare abin da yake wajibi da
nisantar haramce-haramce ya fi yawa
nesa. Ba mamaki a kan haka, domin
kuwa ya fada a cikin Hadisi Qudusi
cewa Allah Ta’ala ya ce: “Bawana ba
zai kusance ni da wani abu da na fi
so ba, kamar abin da na wajabta
masa.” Shi kuma Annabin ya ce a
wani Hadisi: “Allah ba ya da buqata da
Azumin duk wanda ke qarya da aikin
jalilci.” Ko shakka babu, kula tare da
kiyaye wadannan Hadisai guda biyu
ne kawai, za su sa aikin mutum ya
inganta, har ya samu kyakkyawan
sakamako. Kuma matuqar ba haka ya
yi ba, ko ya ce yana koyi da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ne, sai dai
mu saurare shi.
Abin da, da yawa daga cikin musulmi
ke yi a yau, na mayar da hankali ga
kiyaye nafiloli, kamar Sallar Tarawihi,
da yawaita sadaqa, alhali ba su kula
da alfarmar wasu wajibbai ba, kai sun
ma tozartar da wasu; kamar haqqin
uwaye da yin Sallah cikin lokacinta, ko
shakka babu yin haka babbar hasara
ce. Domin kuwa dagewa a kan kare
alfarmar uwar dukiya, ga mai hankali,
ya fi kokawar neman riba, wato saki
sa kama tozo. Sai fa idan an tabbatar
da kammalar wajibban, to ba komai.
Allah ya sa mu dace, amin.
2.3 Tsayuwar Dare:
Tsayuwar dare wata alama ce ta
nagartattun bayi wadanda suka karba
sunan bayin Allah. Kuma tarihi ya
tabbatar da cewa babu lokacin da
Malamai magadan Annabawa wadanda
ke fafutukar gyara halayen al’umma
suka yi sake da tsayuwar dare, a
matsayinsu na masu koyi da Annabi
Sallahu Alaihi Wasallam.
Ko ba lokacin Azumi ba, babu daren
da ke kamawa Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama bai tsayu a cikinsa ba,
balle lokacin Azumin. Akwai Hadissai
da dama da ke bayani a kan yanayi da
sigogin tsayuwar daren Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan
lokaci na Azumi. Ga kaxan daga ciki:
Nana Aisha Raliyallahu Anha ta ce:
“Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ba ya raka’ar da ta wuce
goma sha daya a cikin dare, ko cikin
watan Azumi ko waninsa.” A wani
Hadisin kuma take cewa: “Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan
yi raka’a goma sha uku ne a cikin
dare. Sannan idan an kira Sallar
Subahin ya yi nafila raka’a biyu ‘yan
gajeru.” Ka ga kenan wadannan
hadissai biyu na nuna mana cewa
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
kan yi raka’a goma sha daya ko sha
uku ne kawai a dare.
Bayan wannan kuma, akwai bayanai
daban-daban da suka inganta a kan
yadda yake gudanar da wadannan
salloli. Wanda hakan ke nuna duk
yadda mutum ya zabi yi daga ciki, ya
yi. Duk da yake an fi so, kai ma ka
sassaba, amma kamar yadda
Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, wato
ka rinjayar da yin raka’a biyu-biyu
kana sallamewa, don shi ma haka ya
yi. Allah dai shi ne mafi sani. Amma
dai tabbataccen abu ne a shar’ance
cewa, babu dalilin da zai sa mutum ya
mayar da hankali ga yawaita raka’o’i
barkatai a dare, duk da yake kuwa
akwai lada a cikin yin haka. Amma da
zai tsaya ga tsawaita adadin da
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya
yi, ta hanyar jan dogayen surori da
narkewa a cikin tsoron Allah da
tadabburi da zikiri da addu’o’i fai da
boye, tare da tabbatar cikar ruku’i da
sujada da sauran rukunnan Sallah, to,
da hakan zai fi. Ba laifi ba ne, kamar
yadda muka fada a baya kadan don
mutum ya yi fiye da yadda Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi,
amma dai kar a manta cewar da ya yi:
“Ana tsayuwar dare ne raka’a biyu-
biyu.” Ka ga bai qayyade adadi ko
siga ba.
Abin da ke faruwa a wannan zamani
namu, na sassabawar mutane a cikin
adadin raka’o’in Tarawihi, babu laifi a
ciki. Domin kuwa ba adadin raka’o’i
ba, ko lokacin yin Sallar Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama bai
qayyade mana ba. Ya dai kwadaitar da
mu ne kawai a kan yin ta. Ka ga ke
nan al’amarin na da faraga, ta yadda
kowane musulmi ke iya dibar
gwargwadon qarfinsa, sharadi kawai
shi ne ya yi da kyau. Duk da yake yin
yadda Annabin ya yi, ya fi dacewa.
Kuma shi ma wanda ya yi hakan lalle
ne ya gudanar da Sallar a cikin
cikakkar siga. Allah shi ne masani.
Abin da ya sa muke nanata cewa yin
yadda Annabi ya yi ya fi, shi ne, abu
ne mai matuqar yiwuwa don tsananin
son a yi kandam da lada, musamman
irin dabi’ar nan ta dalibai, ta rashin
sassauci a komai, a je garin neman
qiba a samo rama. Domin kuwa ai
qoqarin koyi da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama na buqatar
taskai.
Wata sigar kuma ta tsayuwar daren
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ita
ce, ba yakan kwashe tsawon daren
yana Sallar ba. A’a, yakan hada ne da
karatun Alqur’ani da kuma wani abun,
kamar yadda Nana Aisha Raliyallahu
Anha ke cewa: “Ban taba sanin Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya karance
Alqu’ani a dare daya, ko ya kai safe
yana Sallah, ko ya share wata cur
yana Azumi in ba Ramalana ba.” Haka
kuma dan Abbas Raliyallahu Anhu ya
ce: “Jibrilu kan zo su yi karatun
Alqur’ani tare da Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama a kowane dare na
Ramalana.” Ka ga ashe ba kwana ya
ke Sallah ba, kenan. Ko shakka babu
wannan tsari na Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama a cikin wannan
ibada, tsari ne mai kyau. Domin kuwa
hakan za ta ba shi damar ba jiki da
iyalinsa haqqinsu, ya kuma gudanar
da ibadar cikin marmari, don kwasar
karan mahaukacciya bai dada komai
ba. Kuma a ci yau, a ci gobe ai shi ne
harka.
Wata siga kuma ta tsayuwar daren na
sa, Sallallahu Alaihi Wasallama ita ce,
yin ta da yake yi shi kadai ransa, ba
tare da jama’a ba, don tsoron kada
hakan ya wajabta Sallar ta Tarawihi a
kan al’ummarsa. Anas Raliyallahu
Anhu ya riwaito, yana cewa: “Wata
rana Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama na Tarawihi shi kadai, sai
na lallabo na bi shi, wani mutum
kuma ya zo shi ma ya bi, da haka dai
har jama’a suka taru. Da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji
alamar jama’a bayansa, sai ya dan
sassauta sallar. Daga nan bai sake
Sallar a waje ba, balle mu bi shi. Da
safiya ta yi muka ce ma sa: “Hala jiya
ka ji mu ne bayanka, shi ya sa ka
koma ciki? Sai ya karba mana da
cewa: “Lalle na ji ku, shi ya sa ma na
yi abin da na yi.” Haka kuma Nana
Aisha Raliyallahu Anha ta ce: “Wata
rana da tsakar dare Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama ya tafi masallaci don
yin Sallah, sai wasu Sahabbai suka bi
shi. Safiya na yi suka cika gari da
labari. A rana ta biyu sai jama’a suka
taru sosai, kuma Annabi ya fita don
Sallar, suka kuma bi shi. Safiya kuma
na yi labari ya qara watsuwa. A rana
ta uku, ba sai masallaci ya cika ba!
Aka maimaita irin jiya. To, ai fa rana ta
hudu da Annabi ya ga irin yadda
masallaci ya cika ya batse, sai ya qi
fitowa, har wasu daga cikin mutanen
suka rinqa cewa: “Lokaci ya yi
Manzon Allah!” Annabi na ji ya qyale
su. Sai da lokacin Sallar Subahin ya
yi, ya fito. Bayan an qare Sallah sai ya
fuskanci jama’a, ya kadaita Allah, ya
ce, “Bayan haka, ku sani ba wulakanci
ya sa na qyale ku jiya ba. Na ji tsoron
ne kada a wajabta maku Sallar dare,
ku kasa.”
Haka kuma Abu Zarrin Raliyallahu
Anhu ya ce: “Mun yi Azumi tare da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama amma, sai da watan ya kai
ashirin da uku sannan ya fara Sallar
Tarawihi tare da mu. A ranar muka yi
ta Sallah har sulusin dare na farko ya
shude. A rana ta ashirin da hudu
kuma sai ya yi Sallarsa shi kadai. Sai
a rana ta ashirin da biyar ya fito muka
yi tare, har zuwa tsakiyar dare. Ganin
haka sai muka ce masa: “Ya Manzon
Allah me zai hana ka ci gaba da ba
mu Sallar nan har daren nan ya qare?.
Sai ya karba mana da cewa: “Ai duk
wanda ya yi Sallar dare tare da liman
to, Allah zai ba shi ladar sauran daren
da bai sallata ba, matuqar limamin ne
ya katse daren.” Mai riwaya ya ci gaba
da cewa: “Daga ranar kuma bai sake
Sallar tare da mu ba. Sai ranar ashirin
da bakwai ga watan, a inda ya gayyato
mata da mutanen gidansa, muka yi ta
Sallah, har sai da muka ji tsoron sahur
ya kubce mana.”
Ko shakka babu wannan irin doguwar
Sallah da Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya jagoranci Sahabbai
koyarwa ce ga al’umma, da kuma
nuna tsananin qaunarsa ga ita
al’ummar, kuma da matsanancin
tsoron da yake da shi, na gudun a
farlanta masu irin ta, wasu daga
cikinsu, su kasa yi, Allah ya kama su
da laifi. Wani abin ban sha’awa kuma
tattare da haka, su kuma Sahabban
sun dage a kan sai ya jagorance su
Sallar fiye da yadda yake yi. Shi kuwa
Sallallahu Alaihi Wasallama yana ta
kakkaucewa, saboda tabbacin da yake
da shi na rauni da kasawar
al’ummarsa Sallallahu Alaihi
Wasallama. Wannan hali da Manzon
Allah ya nuna a wannan lokaci ya
tabbatar da cancantarsa da kirarin da
Allah Madaukakin Sarki ya yi masa a
cikin Alqur’ani da cewa: “Lalle ne,
haqiqa, Manzo daga cikinku ya je
muku. Yana gudun abin da ke wahalar
da ku. Mai kula ne da ku, mai tausayi
ne, mai jinqai ga muminai.” (9:128)
Irin wannan hali na yin tsaye, tsayin
daka a kan ganin ya dora al’ummarsa
a kan tafarki madaidaici, ba kuma tare
da ya takura su ya kai su ga bango ba,
balle hakan ta kai su ga fadawa
tsantsi. Tabbas irin wannan dabi’a ce
ya kamata masu wa’azi da qoqarin
gyara al’umma su yi koyi da ita, ko
suna kai ga gaci.
Sallar Tarawihi, idan muka nazarci
wadannan nassosa da suka gabata, za
mu fahimci cewa tana da matuqar
girma da daukaka. Kuma gudanar da
ita a cikin masallatai Sunnah ne,
domin Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi haka. ‘Yar saurarawar
da ya yi kuma, ya yi ta ne don gudun
kada a farlanta ta a kan al’umma.
Wafatinsa Sallallahu Alaihi Wasallama
ya kawar da wannan fargaba, domin
an nade tabarmar sabunta doka.
Tabbatar wannan aminci ta sa halifa
Umar Raliyallahu Anhu da ya ga
musulmi na yin wannan Sallah daban-
daban, sai ya ce a zuciyarsa: “Me zai
hana in tattara su wuri daya, in sa
wani alaramma ya limance su. Lalle
haka za ta fi dacewa!” Nan take kuwa
sai ya dora wa Sahabi Ubayyu Dan
Ka’abu Raliyallahu Anhu wannan
nauyi.
Wannan kyakkyawan aiki na Halifa
Umar Raliyallahu Anhu ya sami
karvuwa matuqa ga Sahabbai. Saboda
haka ne ma, aka riwaito cewa
Sayyidina Ali Dan Abu Dalib
Raliyallahu Anhu wata rana ya fita da
dare a cikin watan Azumi, ya ga irin
yadda masallatai suka cika da haske,
ba kuma abin da ke tashi sai amon
karatun Alqur’ani. Ganin haka sai ya
ce: “Allah ya haskaka qabarin Umar
xan Haddabi kamar yadda ya haskaka
masallatan Allah da karatun
Alqur’ani.” Ka ga da wannan ya
tabbata cewa, yin Sallar Tarawihi tare
da liman abu ne da ke da falala, kuma
duk mai son alheri ga kansa ba zai
bari ta wuce shi ba, domin Sunnah ce
ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
da Sahabbansa. Ya kuma tabbata,
kamar yadda muka fada a baya kadan
cewa, Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce, Allah na rubuta
cikakkar lada ga wanda ya sallaci
sashen daren Azumi tare da liman,
matuqar limamin ne ya katse daren
amsa ga Sahabban da suka so ya
jagorance su Sallar har qarshen dare.
Allah shi ne mafi sani.
Wannan duka na nuna cewa, abin da
wasu mutane ke yi na qin daurewa su
kammala Sallar Tarawihi tare da
limamin da su ke bi, wai don ya wuce
raka’a goma sha daya, yin haka abu
ne da bai dace ba. Duk da yake
qoqarin biyar Sunnah qeqe da qeqe,
abu ne da ke da lada a wurin Allah,
amma da mutum zai hanqure ya gama
Sallar tare da liman, ko da ya wuce
wancan adadi, hakan zai qara masa
lada ne ba rage ta ba.
Haka kuma wani abin da muke ganin
bai dace ba, wanda kuma ya zama
ruwan dare a yau, shi ne ciratar da
wasu mutane ke yi daga wani
masallaci zuwa wani kullum, ko bayan
wani dan lokaci. Duk da yake a sane
muke da cewa wataqila suna yin haka
ne don cin ribar sauraren karatun
Alqur’ani da wasu limaman ke yi cikin
kyakkyawan sauti fiye da wasu, da sa
tsoron Allah da tadabburi da tsawaita
Sallah da suke yi, wanda hakan ke
taimaka wa mutum ga qara qamewa a
kan ayyukan da’a da taqawa. Amma
duk da haka da za su zavlbi masallaci
daya su riqe, ya fi.
Babban abin da ya sa muka qyamaci
wannan dabi’a shi ne da yawa ake
fara Sallah ba tare da irin wadannan
mutane ba. Ko ma wani lokacin Sallar
ta kubce masu baki daya. Sai dai su yi
ta su kadai, saboda suna can suna
neman masallacin da ake karatu mai
dadi. Wani lokaci ko sun sami irin
wadannan masallatai, sai ka taras
hankalinsu na can ga zaqin karatu ba
ibadar ba. Zancen yin tadabburi a
cikin ayoyi da ma’anonin Alqur’ani, da
kyautata ita Sallar kanta, balle yin
tasiri da ayyukan da ta qunsa bai taso
ba. Amma kuma duk wannan magana
da muke yi ta taqaita ne a kan wanda
ke zaune cikin jama’a, yake kuma da
halin yin Sallar cikin jam’i. Wanda
kuwa ke zaune shi kadai a daji, ko
yana a birni amma wani uzuri ya hana
shi iya halartar jam’in Tarawihi, to, ba
laifi don ya sallace ta shi kadai.
Tabbas kuma zai samu cikakkiyar lada
daga wurin Allah. Domin kuwa Allah
ba ya tilasta wa rayuwa abin da ba ta
iyawa.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s