HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA’I DA KUNCI DA DAMUWA(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Babu ko shakka kowa a yau ya
san al’ummar musulmi a duniya
suna cikin halin kunci da
damuwa, don haka wajibi ne
malamai da daliban ilimi su ci
gaba da haskawa al’umma
hanyoyin da ya kamata su bi don
samun mafita daga wannan
bala’i da musifa. Ga wasu
hanyoyi goma da zamu runguma
da izinin Allah, Allah zai yaye
mana wadannan musifu:
1. Kyautata imani da Allah da
nisantar abin da yake tauye
imani : Allah ya yi alkawarin
taimakon bayinsa muminai, da
basu nasara akan abokan
gabarsu. Don haka matukar
akwai imani da Allah a zukatan
bayi to Allah ba zai tozarta su
ba.
2. Tuba da Istigfari da Komawa
zuwa ga Allah.
3. Yawaita ayyuka na kwarai,
saboda ayyukan kwarai sukan
kawo wa zuciya nutsuwa, kamar
yadda munanan ayyuka sukan
kawo wa zuciya bakin ciki da
damuwa da kunci.
4. Yawaita Sadaka : musammam
ma a boye ba tare da an sani ba,
ya tabbata a hadisi Manzon
Allah S.A.W ya ce “Aikata
kyawawan ayyuka suna kawar da
munanan abubuwa, sadakar
boye tana kawar da fushin
Ubangiji, sada zumunci yana
kara tsawon rayuwa, dukkan
aikin alheri sadaka ne, masu
aikin alheri a duniya, su ne
ma’abota alheri a lahira, masu
munanan ayyuka a duniya, su ne
masu ma’abota mummuna a
lahira, farkon wadanda za su
shiga Aljannah su ne masu
aikata kyawawan
ayyuka”.Dabarani ne ya rawaito
shi.
5. Addu’a : ba don addu’a ba da
mutane da yawa sun halaka.
Allah madaukakin Sarki yana
jarrabar bayinsa da bala’i don su
koma gare shi, su kaskantar da
kai da addu’a, idan suka koma
zuwa gare shi, suka kasakantar
da kai sai ya yaye musu.
6. Umarni da kyakkyawan aiki da
hana mummuna : Allah ba zai
halaka al’umma ba, matukar
akwai masu umarni da
kyakkyawan aiki da hana
mummuna.
7. Nisantar Zalunci : Allah ya
halakar da al’ummu da yawa
saboda zalunci. Mafi girman
zalunci shi ne shirka da kafirci,
sai zaluntar bayin Allah a cikin
dukiyarsu da mutuncinsu da
jininsu, mu nisanci zalunci mu
zauna lafiya.
8. Zikiri wato ambaton Allah, da
baki da zuciya da gabbai. Da
ambaton Allah ne zukata suke
nutsuwa.
9. Neman ilimin addinin
musulunci : Al’umma tana tsira
daga halaka idan akwai malamai
a cikinta, wadanda za su kama
hannunta daga duhu zuwa
haske, daga shirka zuwa tauhidi,
daga bidi’a zuwa sunnah. Duk
al’ummar da ta bar ilimin addini
ta shagala da na rayuwa to tana
tare da kunci da bakin ciki da
rashin kwanciyar hankali.
10. Hakuri da Juriya : Hakuri
wajen bin Allah, hakuri wajen
barin sabon Allah, hakuri akan
abin da Allah ya kaddara, samun
nasara yana tare da hakuri.
Allah ka kara mana hakuri wajen
yi maka da’a, da barin abin da ka
hana, ka yafe mana
kurakuranmu.

Advertisements

2 thoughts on “HANYOYI GOMA DON FITA DAGA BALA’I DA KUNCI DA DAMUWA(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s