KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 36(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


HANYOYIN KYAUTATA WA’AZI
DA YADDA AKE FUSKANTAR DA
SABANI TSAKANIN MALAMAI
Daga: Dr Muhammad Babangida
Muhammad
Al’ummar Musulunci ta kafu ne a
kan harsashin wa’azi. Wa’azi ne
ya haifar da ita, wa’azi ne yake
tafiyar da rayuwarta kuma wa’azi
ne yake fuskantar da alaqarta da
sauran al’ummomi. Manzon
Allah (S.A.W.) ya isar da saqon
Allah ta hanyar gargadi da
wa’azi. Wadanda suka saurari
wa’azinsa suka yi imani da shi su
ne, “Musulmi.” Wadanda suka qi
sauraron sa, suka yi girman kai,
suka qi yin imani da shi su ne
kafirai. Makomar wadancan
aljanna, su kuma wadannan
makomarsu wuta.
Al’ummar Musulmi ta ginu a kan
imani da Allah da ManzonSa tare
da zamantakewa cikin ruhin
soyayyar juna da ’yan’uwantaka
da hadin kai da taimakon juna a
kan ayyukan alheri. Martabar
Musulmi da qarfinsu da
halifancinsu a bayan qasa sun
ta’allaqa da yadda suka riqi
wa’azi da kuma dangantakarsu
da juna.
Kyautata yin wa’azi da samar da
hadin kai da kiyaye ladubban
sabani tsakanin Musulmi suna
daga cikin mafi muhimman
buqatu na kowace al’umma
Musulma. Haqiqa a kowane
zamani al’ummar Musulmi suna
buqatar wa’azi don a mayar da
hankulansu zuwa ga
mahaliccinsu da dalilin halittar
su. Mutane suna buqatar wa’azi
don inganta ibadarsu da
rayuwarsu da kyautata
mu’amalarsu da juna.
Abin takaici ne cewa sabani da
husuma tsakanin Musulmi sun
fadada kuma sun yi muni mai
tsanani, abin da ke jawo koma
baya da yawa a cikin al’amuran
addinin Musulunci a halin da
muke ciki yanzu. Ya dace mu yi
tsokaci a kan wadannan
matsaloli domin samar da
mafita mafi dacewa.
Yana da kyau mu dubi
muhimmancin wa’azi da
qalubalen da ke fuskantar wa’azi
da masu wa’azi a yau da
qa’idojin da suka wajaba masu
wa’azi su lura da su domin
samar da mafi kyan tasiri a cikin
al’umma. Haka kuma yana da
kyau mu fayyace bayani a kan
sabani da dalilansa da
nau’ukansa da ladubban sabani
tsakanin malamai.

Advertisements

4 thoughts on “KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 36(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

  1. Pingback: KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 36 (Sheikh Aliyu Said Gamawa) – Nazeer Mukhtar Danjagale's Blog

  2. Pingback: KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 36 (Sheikh Aliyu Said Gamawa) | Nazeer Mukhtar Danjagale's Blog

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s