NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”02( Dr. Mansur Sokoto)


Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad
Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar
Bahrain da Allah ya ganar da shi
gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.

image

KARAMOMIN SHI’A
Bayan cikawar babban marji’inmu
kuma shugaban Hauza ta Najaf
Ayatullahi Al-Khu’i, an yi wani jerin
gwano a garinmu dauke da makara
don suranta jana’izarsa. Ba mu watse
daga wannan jerin gwano ba sai ga
labari ya yadu cewa, a unguwar Al-
Makhariqa an ga hotonsa a cikin
wata. Kuma duk da yake a cikinmu
babu wanda ya ga haka da idonsa
amma kusan kowa ya gaskata kuma
mutanen garin Manama duk sun ba
da gaskiya ga wannan karama
musamman dai mata. Wani abokina
da nake kusa da shi a taron ya ce
min, wai kuwa kai ka ga wani abu? Na
daga kai na kalli sama na ce ma sa ni
kam ban ga kome ba. Sai ya ce ko ni
ma haka. Sai na ce to, me ya sa kake
ba da himma wajen yada wannan
labari kamar ka gani da idonka? Sai
ya ce, ba ka ganin yadda kowa ya
raja’a ga wannan batu? Ko dukan ka
za su iya yi fa idan ka musanta! Sai
muka bushe da dariya. Ba zan manta
ba wani daga cikin mazauna Manama
da shi ma jita-jitar ba ta gamsar da
shi ba cewa ya yi, to ai ko manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam da ya cika ba mu ji ya
bayyana a cikin wata ba!

ME YA RABA NI DA ADDININ SHI’A?
Ba zai yiwu in yi ma kaina shedar
zama na kirki ba. Amma kuma akwai
wasu ababen da rayuwata ba ta iya
natsuwa da su ba ko dadai. Abubuwa
guda uku ne na dade ina samun
qaiqayi a cikin zuciyata game da su a
addinin Shi’a. Wadannan abubuwa
sun haxa da: zagin sahabbai da cin
mutuncinsu da auren wucin gadi
sannan da kiran wanin Allah don
neman kusanci ko neman agaji da
biyan buqata. Wadannan abubuwa
sun dade suna damu na a cikin
rayuwata har kafin Allah ya yi min
gamon katar da gane gaskiya in koma
ma aqidar Ahlussunna wadanda aka
tashe mu a kan tsananin adawa da
gaba da su.

1. Zagin Sahabbai da Cin Zarafin su;

Kamar ko wane dan Shi’a na tashi ina
qyamar su da ganin laifin su bisa irin
tatsuniyoyin da malamanmu suke
shara mana a kan su. Amma fa ban
taba zagin su irin yadda na ji mutane
suna yi ba. Wannan tun da farko na
tsane shi domin a gani na zagi ba ya
cikin ayyukan alheri. Hankalina ya
kasa yarda cewa, a cikin addini da
kuma ayyukan lada akwai zagi da
dibar albarka ko da kuwa a wurin
najasa kamar yadda fitaccen malamin
nan Muhammad At-Tusirkani yake
cewa a cikin littafinsa La’alil Akhbar:
Ka sani mafi dacewar lokaci da wuri
da yanayin da za a la’ance su shi ne
lokacin kama ruwa. Idan ka zo fitsari
ko bahaya da kuma wurin kawar da
najasa ka yi ta fadi kana maimaitawa
ba tare da qyaqqyaftawa ba, kana
cewa: “Ya Allah ka la’anci Umar
sannan Abubakar da Umar, sannan
Umar da Usman sannan Umar da
Mu’awiyah. Ya Allah! Ka la’anci
A’isha da Hafsa da Hindu da Ummul
Hakam da duk wanda ya yarda da
aikinsu har ranar tashin qiyama.”
Daga nan ne na fara samun damuwa
a cikin wannan addini. Littattafanmu
na da da na yanzu a maqare suke da
zancen kafircin sahabbai da cewa sun
yi ridda bayan cikawar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam.
Daga nan kuma sai aka gina la’antar
su da barranta daga gare su. Dubi
abin da ya zo a cikin Rijal As-Kasshi
daga Hanan dan Sudair daga babansa
daga Abu Ja’afar Alaihis Salam cewa:
“Mutane duk sun yi ridda bayan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam in ban da mutane
uku. Sai na ce ma sa su wane ne
ukun? Ya ce, Miqdad dan Aswad da
Abu Dhar Al-Ghifari da Salman Al-
Farisi.” Waxannan su ne wadanda
suka ki yarda su yi ma Abubakar
mubaya’a har sai da aka zo da Imam
Ali aka tilasta shi yin mubaya’ar.
Wasu ruwayoyi sun qara mutane hudu
a cikin wadanda suka tsayu a kan
musulunci ba su yi ridda ba, sai
adadin ya kai bakwai, amma bai wuce
hakan ba. Wannan shi ne abin da
ruwayoyin suke kawowa. An karbo
daga Al-Haris dan Mughira An-Nasri
ya ce, na ji Abdulmalik dan A’ayan
yana tambayar baban Abdullahi
Alaihis Salam, yana ta tambayar sa a
kan wannan har sai da ya ce, kenan
dai mutane duk sun halaka gaba
daya? Ya ce, eh wallahi dan A’yan.
Mutane sun halaka ga baki daya. Ya
ce ma sa na gabas da na yamma? Ya
ce, ai duk sun afka cikin bata, sun
halaka sai mutane uku kawai. Sa’ann
nan daga baya Abu Sasana ya riske
su.
Addu’ar da ake kira “Du’a’u Sanamai
Quraish”; Addu’ar gumakan
Quraishawa biyu da ire-irenta
wadanda suke cike da la’antar
muqarraban manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa’alihi Wasallam Abubakar da
Umar duk sakamakon wancan tunanin
ne da aka gina shi a kan wadancan
rubabbun ruwayoyi da suka ci karo da
Alqur’ani.
Akwai wani lokaci da na tsaya kurum
na nazarci ayar Alqur’ani in da Allah
Tabaraka Wa Ta’ala yake cewa:
“Kuma da wadanda suka yi gabaci na
farko daga muhajirai da ansarai da
wadanda suka bi su da kyautatawa,
Allah ya yarda da su, kuma sun yarda
da shi, kuma ya yi ma su tanadin
gidajen aljanna wadanda qoramu ke
gudana a qarqashin su, suna
madawwama a cikin su har abada,
wannan shi ne rabo babba”. Suratut
Taubah:100
Sai na ga cewa fa wannan aya ta
bayyana qarara yadda Allah Tabaraka
Wa Ta’ala ya nuna amincewarsa ga
magabatan musulmi da suka hada da
muhajirai da ansarai, cikin su kuwa
har da irin su Abubakar da Umar da
Usman da Dalhatu da Zubairu da
Sa’adu dan Abu Waqqas da Abdullahi
dan Mas’ud da Sa’adu dan Mu’azu da
duk wanda ka ga damar ka qirga a
cikin su wadanda a yanzu haka ‘yan
Shi’a suke debe ma albarka.
A nan ne na tambayi kaina cewa, ya
za ayi sahabban annabi su zalunci Ali
Radhiyallahu Anhu su qwace ma sa
haqqen shugabanci ga su kuwa su ne
Allah ya shelanta ya yarda da su har
ya yi ma su tanadin gidajen aljanna?!
Idan dai har manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa’alihi Wasallam ya cika yana
mai amince mu su, kuma Alqur’ani ya
sanar da yardar Allah madaukakin
sarki a gare su, to, ta ya ya za su ja
da baya su lalace; su fada cikin fitina
kai tsaye bayan cikawar maigidansu?!
Ya kuma za ayi wadannan su canja
littafin Allah, su yi ma hukunce-
hukuncen addini gyaran fuska?! To,
wai kam tun farko Allah ya san za su
canja ne su ja da baya ko kuwa ya
ya? Domin kuwa duk musulmi ya
yarda cewa, Allah ya san jiya da yau
da gobe, ba abin da yake boyuwa a
gare shi. To, idan kuwa Allah ya sani
mene ne matsayin ayoyin yabo da ya
saukar a kan su? Idan har malaman
Shi’a ba suna son su ce madaukakin
sarki ya cuci musulmi ba ne da ya
saukar da ayoyin yarda a gare su
kuma ya sanya surukuta a tsakanin su
da manzonsa suka aurar da ‘ya’yansu
gare shi suka kuma auri nasa ‘ya’yan
alhalin ya san cewa munafukai ne, da
zasu yi ridda. Idan ba haka malamn
Shi’a nufi ba to, mene ne manufarsu?
Me ya sa Allah mafaukakin sarki bai
fadi gaskiyar lamarinsu ba in haka ne
don a sani? Rashin samun
gamsasshiyar amsa ga wadannan
tambayoyi ya ja ni zuwa fahimtar
cewa, Allah ya amince ma su
amincewa ta har abada kuma ba zai
bari su ja da baya ba tun da ya furta
kalmar amincewa a gare su. Kuma ya
sani – a cikin iliminsa na azaliyya –
cewa, za su ci gaba da bin tafarkin da
fiyayyen halitta ya dora su a kan sa
ila yaumil qiyamati. In ba haka ba da
babu yadda za ayi ya rubuta a mafi
tsarkin littafinsa cewa ya yarda da su.
Kamar yadda ya fada a wata ayar:
“Haqiqa, Allah ya yarda da mummunai
a lokacin da suke yi ma ka caffa a
qarqashin bishiyar nan, sai Allah ya
kalli abin da ke cikin zukatansu, sai ya
saukar da natsuwa a gare su, ya saka
ma su da budi na kurkusa. Suratul
Fathi:18
“Wadanda kuwa Allah ya ba mu
labarin ya kalli abin da ke cikin
zukatansu, a sakamakon haka har ya
saukar da natsuwa akan su, ba ya
halalta wani ya sa shakku cikin
lamarinsu.”
Cigaba a darasi na uku

Advertisements

2 thoughts on “NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”02( Dr. Mansur Sokoto)

  1. Pingback: NURUN ALA NUR“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMASAHABBAI”02( Dr. Mansur Sokoto) | daawah Salafiyyah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s