NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”03( Dr. Mansur Sokoto)


Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad
Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar
Bahrain da Allah ya ganar da shi
gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.

image

Cigaba

ME YA RABA NI DA ADDININ SHI’A?

2. AUREN WUCIN GADI (Mut’ah)

Shi dai wannan aure duk da yake mun
tashi mun tarar ana yin sa, ana kuma
halasta shi, kai har ma ana sanya shi
cikin aikin lada, da dai zuciyata ba ta
natsu da shi ba. Tun kafin na san
dalilan haramcinsa sau da yawa
nakan ce da mutum a cikin
tattaunawa “kana son a yi da
qanwarka”? Kafin ya ba ka amsa sai
ka ga nan take ya fusata. Wato dai a
aqidance mun yarda da shi amma a
birnin zuciyarmu muna jin ba dadi!
Gaskiyar magana ita ce, an taba
halasta wannan auren a wani dan
quntataccen lokaci a zamanin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam bisa kamawar uzuri da
lalura, daga bisani kuma aka shelanta
haramcinsa har zuwa ranar alqiyama.
Wannan ya zo qarara a cikin
ingantattun riwayoyi daga manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam. Abin ban mamaki ma shi
ne yadda ruwayoyin Ahlulbaiti amincin
Allah ya tabbata a gare su suka
bayyana muni da haramcin wannan
aure da zargin ma su yin sa. Amma
idan ka bijiro da su ka ce, me ya sa
ba mu aiki da wadannan riwayoyin sai
ka ga malami ya turo ma ka hajar
mujiya. Ba zai ce ma ka uffan ba. Ga
kadan daga cikin irin wadannan
riwayoyin:
√ An karbo daga Abdullahi dan Sinan
ya ce, na tambayi baban Abdullahi
Alaihis Salam game da hukuncin
auren Mut’ah, sai ya ce, “kada ka
qazanta kanka da shi”.
Ali dan Yaqdin ya tambayi Abul Hasan
Alaihis Salam game da auren Mut’ah
sai ya ce ma sa: “me ya hada ka da
shi? Allah ya raba ka da shi”.
√ An karbo daga baban Abdullahi
Alaihis Salam cewa, babu masu yin
auren Mut’ah a wurinmu sai fajirai.
Ad-Dusi a cikin Al-Istibsar ya ruwaito
daga Amru dan Khalid daga Zaid dan
Ali daga iyayensa daga Ali dan Abu
Dalib Radhiyallahu Anhu cewa, annabi
Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam ya
haramta cin naman jakan gida da
kuma auren Mut’ah.
→ Duk da ingancin wannan riwaya
sharhin da Dusi ya yi ma ta kawai shi
ne cewa, “Dole ne mu dauki wannan
riwaya a matsayin cewa, an fade ta ne
bisa taqiyya (waskiya) domin ta dace
da riwayar amawa (Ahlus-Sunna). To,
ka ji fa! Ali dan Abu Dalib
Radhiyallahu Anhu wai, ya yi ma
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam qarya da sunan
taqiyya!!
3. TUFKA DA WARWARA A CIKIN
ADDININ SHI’A:

A lokacin quruciya mun saba da raya
dararen Ashura da kuka da marin
fuska da yanka jiki muna tuna kisan
sayyidi Husaini Alaihis Salam amma
da dai rana ba mu taba tsayawa mu yi
tunanin hujjar yin haka a addini ba.
Shin wai Allah ne ya yi umurni da
haka ko manzonSa? Ko kuwa dai
lamarin son zuciya ne kawai?
Malamanmu ba za su taba bari
hankalinmu ya je can ba. Ina! Dubi
irin fatawar da Tibrizi ya bayar da aka
tambaye shi mene ne hujjar makokin
Husaini Alaihis Salam da ake yi?
Kuma ko imamai sun koyar da yin sa?
Ga amsar da ya bayar:
“A da can Imaman Shi’a sun rayu a
zamanin da ake yin taqiyya, babu
‘yancin bayyana ra’ayi saboda tsoro.
Saboda haka ba a hujja da lokacinsu
don ba su samu dama ba, da sun rayu
a irin zamaninmu da babu shakka za
su yi wadannan makokai saboda
alamomin addini ne kamar yadda
muke yi, kamar kafa baqar tuta a
qofofin gidaje da cibiyoyin addini don
bayyana baqin ciki. Yin haka yana da
kyau”.
To, ka ga a nan ba wata hujja sai son
zuciya. Ba umurnin Allah ba ne ba na
manzo ba, ba kuma wani Imami da ya
ce ayi haka. Amma kuma ana kiran
haka wai, raya addinin Allah ko
alamomin addininsa.
Idan ka yi duba da kyau za ka samu
riwayoyin imamai da tsofaffin
malaman Shi’a sun ci karo da wannan
sabon addini da ‘yan Shi’a a duniya
suke yi. Ga wasu ‘yan misalai kadan:
√ Ibnu Babawaihi Al-Qummi ya riwaito
cewa, yana daga cikin kalaman
annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam da ba wanda ya riga shi
fadar su cewa, “Kukan mutuwa na
cikin al’amurran jahiliyya”.
Ad-Dabarsi ya riwaito daga Ali Alaihis
Salam cewa, “abubuwa guda uku na
cikin lamurran jahiliyya wadanda
mutane ba za su daina su ba har
ranar tashin qiyama: neman ruwan
sama ta hanyar duba taurari da sukar
asali da dangantakar mutane da kuma
kukan mutuwa”.
Ba wannan ce kadai ba, akwai wasu
riwayoyin wadanda za mu kawo su a
darasi na gaba da yardar Allah. A
kasance tare da mu.

Advertisements

One thought on “NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”03( Dr. Mansur Sokoto)

  1. Pingback: NURUN ALA NUR“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMASAHABBAI”03( Dr. Mansur Sokoto) | daawah Salafiyyah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s