NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”04( Dr. Mansur Sokoto)


Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad
Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar
Bahrain da Allah ya ganar da shi
gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.

image

Cigaba
ME YA RABA NI DA ADDININ SHI’A?

3. TUFKA DA WARWARA A CIKIN
ADDININ SHI’A

.. Muna kan bayani akan makokin
Husaini Alaihis Salam da tunka da
warwarar malaman shi’a a cikinsa…
√ Majlisi ya riwaito daga Ali Alaihis
Salam cewa, lokacin da Allah ya karbi
ran Ibrahim dan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam,
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam ya umurce ni in yi
ma sa wanka in sa ma sa likkafani da
turare, sannan ya ce in dauko shi
zuwa Baqi’a in da ya yi ma sa sallah.
A lokacin da ya gan shi a kafe sai
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam ya fashe da kuka.
Mutane kuwa duk sai suka yi ta kuka
har muryoyinsu suka daukaka
mazansu da mata. A nan ne sai
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam ya hane su hani
mai tsanani. Ya ce, “idanu suna kuka,
zuciya tana damuwa amma ba za mu
furta kome ba sai wanda yake yardar
da Allah madaukakin sarki. Lalle, mun
shiga damuwa da rashin ka, lalle
muna cikin baqin ciki..”.
Dubi yadda lamari ya canja daga
zaman makoki na cikin ayyukan
jahiliyya – kamar yadda manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam da
sayyidi Ali Radhiyallahu Anhu suka
fada. A yanzu sai aka mayar da
makoki cikin alamomin addini! Saboda
hujjojin da suka hana makoki sun yi
yawa kuma sun zama qarara Dusi da
Ibn Hamza suka bayyana haramcinsa.
Dusi ma cewa ya yi malaman
zamaninsa duk sun hadu a kan
haramcin sa.
Haka kuma riwayoyi sun bayyana
cewa, marin fuska da dukan qirji na
cikin bidi’oin da Allah da manzo ba su
yarda da su ba bale kuma imamai.
Imam Al-Baqir Alaihis Salam yana
cewa, mafi tsananin raki shi ne
hargowa da kiran wayyo Allah da
marin fuska da dukan qirji da cire
gashin kai. Kuma duk wanda ya yi irin
wannan to, bai yi haquri ba, sannan
ya kauce ma godaben shiriya”.
Sai kuma riwayar da aka karbo daga
sayyidi Husaini Alaihis Salam a
lokacin da yake wasici ga ‘yar uwarsa
Zainab yana cewa:
Ya ke yar uwata! Ki ji tsoron Allah. Ki
yi makoki irin wanda Allah ya yarda da
shi. Ki sani duk halittun da ke bisa
doron qasa za su mutu, na sama ma
ba za a bar su ba. Ko wane mai rai
sai ya dandani mutuwa in ban da
ubangiji kadaitacce mahalicci, wanda
ya qaga halittar bayi ya hukunta ma
su mutuwa da tashi a bayan ta cikin
ikonsa. Ki sani mahaifana da dan
uwana – Al-Hasan – duk sun fi ni.
Kuma duk wanda ya rasa wani abin
qaunarsa ya tuna rashin da muka yi
wa manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa’alihi Wasallam.
Sa’an nan ya qara ma ta da cewa:
Ya ke yar uwata! Ina hada ki da Allah,
idan na mutu kada ki yaga tufa, kada
ki mari fuska, kada ki yi ihu ko ki ce
wayyo Allah.
Wannan ne ya sa Muhammad dan
Makki Al-Amuli wanda aka fi sani da
As-Shahid Al-Awwal ya cirato daga
Dusi cewa, mari da yanka jiki da cirar
gashi duk haramun ne saboda suna
nuna qin yarda da qaddara da fushi
da yin Allah. Haka ya kawo shi a cikin
Al-Mabsud.
Sanya baqaqen kaya shi ma laifi ne
kamar yadda zancen sayyidi Ali
Alaihis Salam yake nunawa in da ya
ce: “Kada ku sanya baqaqen tufa
domin irin suturar Fir’auna ce.”
To, ka ji irin dalilan da suka ta da
hankalina a kan abin da na tashi na
tarar ana yi kuma aka koya mana a
ranakun makoki wanda a da muka
dauka cewa ibada ce mai girman
lada. Sai ga shi da muka yi karatu
mun gano cewa wata bidi’ah ce da
take hannun riga da tafarkin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi
Wasallam da iyalan gidansa.
A haduwa ta gaba za mu ji wani
sababin na gaba da ya raba sheikh da
addinin shi’a!

Advertisements

3 thoughts on “NURUN ALA NUR “BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”04( Dr. Mansur Sokoto)

  1. Allahj kashiryi yan uwannan namu sudaina walan banza domin abindasukeyi ba ibada bane bidi ace tsagwaronta ,mukuma Allah yakara kiyayemu

  2. Pingback: NURUN ALA NUR“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMASAHABBAI”04( Dr. Mansur Sokoto) | daawah Salafiyyah.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s