NEMAN ZABIN ALLAH.


istikhara

Ba duk abinda kake maatukar sonsa shi ke zame maka alheri ba akowani lokaci, zai iya zama kaso abu akarshe ya zamto maka sharri. saboda haka aduk lokacin da kaga kana son abu ka nemi zabin Allah acikinsa, domin kada abin ya zamto maka nadama nan gaba….

Allah(subhanahu wata’ala) yace:

وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ.

zai yiwu kuso wani abu wannan abun kuma sharri ne a gareku,sannan kuma zai yiwu kuki wani abu wannan abun kuma ya zamto alkhairi a gareku, Allah shine masani ku baku da sani.surat baqara.

sannan Allah ya sake cewa a wani wuri,

فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا

zai yiwu kuQi wani abu Allah kuma ya sanya alkhairi mai yawa acikinsa. surat nisa’i.
saboda hakane ya dace ko meye musulmi zaiyi ya zamto yana neman zabin Allah aciki, kada yayi gaban kansa. domin a karshe zaiyi nadama. shi yasa an rawaito daga sahabin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) jabir ibn Abdullah(radiyallah anhu) yace manzon Allah ya kasance yana koyar damu neman zabin Allah(istikhara) cikin kowani lamuranmu, kaman yanda yake karantar damu surah acikin alQur’ani. idan dayanku yayi niyyar aiwatar da wani abu, to yayi raka’a biyu wadda ba ta farilla ba,sannan yace:

اللهم إني استخيرك بعلمك، وأستقدرك بقدرتك، وأسالك من فضلك العظيم، فإنك تقدر ولا أقدر، وتعلم ولا أعلم، وأنت علام الغيوب، اللهم إن كنت تعلم أن هذا الأمر خير لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري، فاقدره لي ويسره لي ثم بارك لي فيه، وإن كنت تعلم أن هذا الأمر شر لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري، فاصرفه عني، واصرفني عنه، واقدر لي الخير حيث كان ثم رضني به.

zai fada bukatarsa wurin fadinsa

اللهم إن كنت تعلم أن هذا الأمر
sai ya fadi bukatarsa. toh insha’Allah in mutum ya dage dayin istikhara acikin lamuransa bazai rinka yin danasani ba. Allah taimakemu.

4 thoughts on “NEMAN ZABIN ALLAH.

  1. “Istikhara” means to seek goodness from Allah (Exalted is He), meaning when one intends to do an important task they do istikhara before the task. The one who does the istikhara is as if they request Allah Almighty that, O the Knower of Unseen (Exalted is He) guide me if this task is better istikhara ki dua

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s