NURUN ALA NUR FITOWA TA 6 (Dr. Mansur Sokoto)


10590561_787634704632100_7272317524640159774_n

“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”

“Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.”

BABBAN GINSHIKIN SHI’A YA GANTALE.
Duk wanda yake nazari a cikin addinin Shi’a da sauqi zai fahimta cewa, aqidar Imama wadda a kan ta suke gina so da qin mutane, kuma a kan ta suke amincewa da musuluncin mutum ko su kafirta shi. Wannan aqida ba ayi naqudar ta ba sai bayan rasuwar wanda suke ce ma Imami na sha daya Al-Hasan Al-Askari. A wannan lokacin ne suka rabu gida-gida, aka samu ‘yan sha biyu da ‘yan Isma’iliyya da sauran su. Kafin haka, duk ‘yan Shi’a abin da ya dame su shi ne tawaye a kan sarakunan Banu Umayya da na Banul Abbas. Babu wanda ya san cewa akwai imamai goma sha biyu a lokacin. Wannan ya sa duk wanda ya yi fito-na-fito da masu sarauta a wancan lokaci ‘yan Shi’a suke goyon bayan sa. Kamar yadda suka goyu bayan Zaid dan Ali haka suka goyu bayan Zun-Nafs Az-Zakiyya.

Bari mu dan taba magana a kan abin da ya faru bayan kisan sayyidi Husaini. Shi dai Ali dan Husaini Zainul Abidin – wanda suke ce ma imami na hudu – gaba daya qaurace ma harkokin mulki da siyasa ya yi, ya himmatu wajen ibada. A kan haka aka san shi da tsentseni da yawan salla. Har ma shehunan malamai irin su Al-Mufid da Arbili suka riwaito cewa yana salla raka’a dubu a kowace rana. Kuma duk ruwayoyinsa idan ka bibiye su ba su wuce wa’azi da addu’oi da hikimomi na rayuwa. Maganarsa a hukunce-hukuncen shari’a qalilan ce qwarai. Wannan karon batta da ke tsakanin matsayin da ya dauka da wanda ‘yan Shi’a suke son su dora shi a kai ya kai su ga qaga labarai na yabo da bajintarwa da karamomi duk dai don a tabbatar da shi a matsayin Imam. Amma a lokacinsa ba wata rawa da ya taka a fagen shugabanci. Kawai dai shi mai ilimi ne da matsayi a wurin jama’a kamar ire-irensa amma ba jagora ko shugaba ba.

Dansa Zaidu dan Ali – wanda Zaidiyya ke riqo a matsayin Imami na biyar – ya yi mamaki matuqa a lokacin da ya zo Kufa ya ji ana cewa mahaifinsa imami ne, aqidar da wani da ake ce ma Mu’min Ad-Daq (ko kuma Shaidan Ad-Daq) ya yada a garin. A zantawar da suka yi da shi ya tambaye shi cewa, ya aka yi duk zamana da mahifina bai taba fada min haka ba alhalin tare da shi nake cin abinci har yakan dauko loma ya ajiye min a gabana?. Yakan kuma dauko loma mai zafi ya huce ta sannan ya ba ni! Ya aka yi yake ji min tausayin zafin tuwo amma bai ji ma ni tausayin wutar lahira ba har ya karantar da kai wannan ni ya boye min shi?! Amsar da Shaidan Ad-Daq ya ba shi ita ce: “Allah ya sanya ni in zamo fansarka. Bai gaya maka ba ne don yana tausayin wuta a gare ka. Saboda idan ya gaya ma ka ba ka yi imani ba za ka shiga wuta. Ni kuma ya gaya min don bai damu ba, in na gaskata in tsira in ba haka ba in shiga wuta ba ruwansa. Kamar yadda annabi Ya’qub ya boye mafarkin dansa Yusuf bai fada ma sauran ‘ya’yan ba!”.

To, ka ji fa! Wai dan Imam ma bai sani ba har baban na sa ya rasu suna can Madina, sannan a qasar Iraqi ya tsinci labarin daga wurin wani Shaixan Ad-Daq.
Wannan wani bangare ne na tarihin Shi’a da bai kamata ayi fatali da shi ba. Akwai wasu abubuwa da ke warware aqidar tun daga tushenta. Za mu dan fadi wasu daga cikin su.

Akwai wasu hadissai da ke nuna cewa, ana iya samun imami amma duk ‘yan Shi’a ba su san shi ba. Kuma har a shata ma su mafita idan haka ta faru. Wanda kuwa duk ya san yadda aqidar imamanci take a wurin su ya san hakan ba za ta yiwu ba. Domin kuwa wajibi ne ga ko wane dan Shi’a ya san imamai goma sha biyu da sunayensu da asalinsu.
Kulini ya riwaito cewa, wani mutum ya tambayi Baban Abdullahi Alaihis Salam: Idan na wayi gari na maraita ban ga imamin da zan yi koyi da shi ba ya zan yi? Sai ya ce, “ka so duk wanda ka ga dama, ka qi duk wanda ka ga dama har Allah ya bayyanar da shi.”
Saduq shi kuma riwaya ya yi daga Imam As-Sadiq Alaihis Salam yana cewa: Ya ya za ku yi idan kuka dauki wani lokaci ba ku san imaminku ba? Sai aka ce ma sa, to ya ya za mu yi? Sai ya ce, “ku riqa na farkon har na biyun ya bayyana.”
Haka kuma Kulini da Saduq da Mufid duk sun riwaito daga Isa xan Abdullahi Al-Alawi Al-Umari ya tambayi baban Abdullahi; Ja’afar dan Muhammad As-Sadiq Alaihis Salam, ya ce ma sa: “Allah ya sanya ni fansar ka. Idan Allah ya sa aka wayi gari wata rana ban gan ka ba da wa zan yi koyi? Sai ya nuna Musa (Al-Kazim). Sai na ce, to, in ya wuce fa? Sai ya ce, ka yi koyi da ‘ya’yansa. Sai na ce, to idan suka mutu suka bar dan uwansu babba da dansu qarami da wan ne zan yi koyi? Sai ya ce, da dan zaka yi koyi. Kuma haka zaka riqa yi har abada. Sai na ce, to idan ban san shi ba kuma ban san in da shi ke ba ya zan yi? Sai ya ce, ka ce: “Ya Allah! Ina jibintar duk wanda ya rage daga cikin hujjojinka cikin ‘ya’yan imamin da ya gabata”. Idan ka yi haka ya ishe ka.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s