NURUN ALA NUR FITOWA TA 7 (Dr. Dr. Mansur Sokoto)


“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI”

“Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.”

BABBAN GINSHIKIN SHI’A YA GANTALE (2)

Akwai kuma wasu riwayoyi masu yawa daga Zuraratu dan A’ayan da Ya’qubu dan Shu’aib da Abdul A’ala duk sun tambayi Imam As-Sadiq cewa, idan wani abu ya faru ga imami ya mutane za su yi? Sai ya ce, su yi kamar yadda Allah ya ce:

“Ina ma da wata qungiya daga cikin kowannen su ta fita don ta karanci addini..” zuwa qarshen ayar. Sai na ce, to mene ne halinsu? Sai ya ce, suna da uzuri. Sai na ce, Allah ya sanya ni fansar ka. Masu jira ya za su yi kafin masu yin karatu su dawo? Sai ya ce, Allah ya jiqan ka, kai ba ka san cewa a tsakanin annabi Isa da annabi Muhammad akwai shekaru dari biyu da hamsin ba? Ai wasu sun mutu a kan addinin annabi Isa suna jiran annabi Muhammad, don haka Allah ya ba su lada ninki biyu. Na ce, to idan mun tafi sai wasu suka mutu a hanya fa? Sai ya karanta min ayar: “Wanda duk ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da manzonsa sannan mutuwa ta riske shi to, ladarsa ta tabbata a wurin Allah”. Na ce, to idan mun isa a garin mun tarar Imam ya kulle gidansa ya shige ya zamu yi? Ya ce, wannan lamari fa ba ya kasancewa sai da lamari bayyananne. Shi ne wanda idan ka shiga a gari ka ce ina wanda wane ya yi ma wasici? Za a ce ma ka ga shi nan.
Riwayoyi da yawa kuma sun nuna yiwuwar a samu imamin da shi ma bai san kansa ba. Ko kuma bai san imamin da zai gaje shi ba sai kusan mutuwarsa. A bayan ko wane imami sai ‘yan Shi’a sun rikice a game da wanda zai gaje shi. Sukan zo wurin wanda suka ce shi ne imam suna magiya ya fada ma su wanda zai gaje shi kuma duk da haka sai sun shiga rudani da rikici a bayan mutuwarsa.
Akwai babi a cikin littafin Basa’ir Ad-Darajat na Abu Ja’afar As-Saffar – daga cikin almajiran Imam Al-Askari – wanda aka sa ma sa suna kamar haka: Babi Mai Bayyana Cewa, Imamai Sun San Wanda za su yi ma Wasici Gabanin Mutuwarsu Daga Cikin Abin da Allah ya Sanar da su. A cikin wannan babi malamin ya kawo riwayoyi masu tarin yawa, cikin su har da wacce ya karbo daga AbdurRahman Al-Khazzaz daga baban Abdullahi Alaihis Salam cewa, Isma’il dan Ibrahim yana da wani da qarami da yake matuqar kauna, kuma ya yi fatar ya yi ma sa wasicci da imama, sai Allah bai yarje ma sa ba. Allah ya ce ma sa wane dai ne. A lokacin da mutuwa ta zo ma sa, wasiyyinsa ya zo sai ya ce ma sa, idan mutuwata ta zo ga yadda za ka yi. Daga nan ne duk wani imami da zai cika sai Allah ya sanar da shi wanda zai gaje shi. A cikin wannan littafin da muka fada har wayau, akwai babi mai taken: Babi Mai Bayyana Cewa, Imami ya San Wanda Zai Gaje Shi Kafin Mutuwarsa.

Wannan rashin tabbas da yake tattare da aqidar imama a wurin ‘yan Shi’a wanda ya kai ga ko imami bai san mai gadon sa ba sai ya zo mutuwa ya dada shigar da rudani a tsakanin ‘yan Shi’a da sanya su hauragiya a tsakanin mutanen da suke tuhumar imamancin ya fada a kan su. Misali, har a lokacin da Zuraratu dan A’yan ya cika bai san wane ne imami a bayan Sadiq ba, alhalin ya yi zamani da zamantakewa da Sadiq da babansa Baqir dukan su.

Zuraratu ya aiki dansa Ubaidullahi daga Kufa ya je Madina don ya shaqo ma sa labarin wane ne imami na gaba? Amma sai mutuwa ta riske shi kafin dan nasa ya dawo. Don haka, ya dauko Alqur’ani ya dora a qirjinsa yana cewa, “Ya Allah! Ka sheda cewa, ina biyayya ga duk wanda Alqur’anin nan ya tabbatar da imamancinsa.”

Ka ga kenan da ya san cewa, Musa Al-Kazim shi ne imami na gaba a wancan lokaci da bai bukaci sai ya aiki yaronsa ba don ya nemo ma sa bayani. Da kuma bai shiga rudani da kokwanto a kan matsalar ba.

Advertisements

One thought on “NURUN ALA NUR FITOWA TA 7 (Dr. Dr. Mansur Sokoto)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s