TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)


Jawabin da Malam Dahiru
Bauchi ya yi a shirin safe na BBC
hausa a yau 21/5/2015, hakika
ya fadi daidai cikin wani sashi
nasa, ya kuma kasa fadin daidai
cikin wani sashi nasa.Ya fadi daidai a inda ya kafirta
‘yan Tijjaniyyar nan da suka yi
bukin maulidin Sheik Ibrahim
Inyas a garin Kano, sannan a
wajen wannan buki nasa
wasunsu suka yi ta furta
kalaman batunci ga Annabi Mai
tsira da amincin Allah.
Amma bai fadi daidai ba a inda
ya ce babu abin da ake kira Ahlul
Hakikati cikin Darikar Tijjaniyyah,
ya kuma fadi hakan ne duk kuwa
da cewa a cikin Darikar tijjaniyyah
a kwai yarda da abin da ake kira
Wahdatul Wujudi, shi kuwa
Wahdatul Wujudi tabbas yana
daga cikin lazimin wannan akida
yarda da irin maganar cewa
Ibrahim Inyas Allah ne.
Ko shakka babu a cikin darikun
Sufaye musamman Darikar
Tijjaniyyah a kwai gurbatattun
akidu daban daban na tozarta
Alqur’ani, da tozarta Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah,
da ma tozarta Zatin Allah shi
kanSa, hakika dukkan masu
nazarin littattafan wadannan
darikun sun san da haka.
To amma dai a takaice muna iya
cewa an dan samu ci gaba cikin
jawaban da shi Malam Dahiru
Bauchi ya yi; domin a da irin
wannan bayanin ne na bayyanar
da kafircin wasu akidu na Sufaye
idan Ahlus Sunnah masu
Da’awah suka bayyana su ga
Duniya zai a ji wasu daga cikin
masu gafala ko son zuciya suna
ta cewa: ‘Yan Izala na kafirta
Musulmi!
Muna fata Malaman Sufaye a ko
ina suke za su yi hakuri, su kara
tunani su sa tsoron Allah cikin
lamuransu su daure su yi
Musuluncin nan kamar yadda
Annabi Mai tsira da amincin
Allah tare da Sahabbansa suka yi
shi. Allah Ya taimake mu.
Ameen.

Advertisements

16 thoughts on “TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

  1. Allah ya saka da alkhairi malam sulaiman adam sabo da tunatarwar da kaiwa wannan azzalumi,dan son zuciya wato jalo jalingo kan irin mummunar akidar su ta kin ahlulbaiti da kafirta masoyan shugaba(saw)wato yan darikun sufaye.Bayan haka kai kuma jalingo ka manta fadin Gumi cewa gara kirista da musulmi dan darika,da cewa jefa kuri’a yafi sallah?

  2. Allah Yashirya yan izala idan sunada rabon shiriya a kullun basuda aiki sai karya da kafirta yan darika kuma kusani cewa wallahi yan darika sunfi karfinku makiya manzon Allah (SAW) kai Allah ya tsine maku Kuma da sannu duk sai Allah Ya halakar daku dakuda mabiyanku

  3. Hm haba jalo jalingo harkana da bakin magana anan kamanta Zagin da kayiwa syd Aliyu bin Abidalib kamanta zagin da Ibni taimiya yayiwa syd Nana Kadija da Syd Nana Fatsuma Acikin Littafinsa Minahaji sunnah Kamanta fatawawar sa akan ziyarar Annabi S.A.W.kumakamanta Gumi dayace yan Darika kafiraine ai ba yanhakika yaceba Amdayake Bakada Adalci kajimaganar da kakae fada

  4. Malan Usman Ai ba fada bane kamar yanda malan jalo jalingo ya fadi hujjo Jin shi bai yi zagi ba hujjoji ya fada sai ka fadi hujjan ka kuma ka fadi littafin da ka dogara da shi kuma ka fadi shifin da yake kuma ka sani fa mai Abun fada baya fada Mara Abun fada shi yake fada Allah ya kara shiryadda mu Ameen

    • aikowa yasan yan,izal arnane kuma kafiraine kuma cinmatan mutane suke amasallahci kaiwawa dakake izala bakasan meyake faruwa kaje kai bincike akan izala kuma menene izala.inaso dan izala yaje yaibincike akan izala kafin yasan mene mah izalarma. mumun san maye sunnar tasu bawata bace illah fasukanci damatan mutane dan izalah kai badan sunnabane,saidai kace kai dan ahalil sunsunanekai shine zamu yarda dakai.idanko hakane to munyarda.dama kun ce akoyawa mata karatu agida kafircine ammah mutane sukawo matansu masallahci kucisu wannan sunnane kai yan,izahla wallahi kunji kunya.matsiyata sunannu iyalan fir auna da hamana.

  5. Kaiko jalo makaryacine adarika wallahi bawasu yan hakika hasalima shehu yayi risalatul muntakimu jalon jahilai baamagana sai anyi bincike

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s