Raddin Abduljabbar dan Taratsi Ga Mulhidan ‘Yan Tijjaniyya


Assalamu Alaikum Barkanku da yau. Kaman yanda kowa ya sani ne cikin kwanakinnan muna cikin bakin ciki game da abubuwan da wasu ‘yan tijjaniyyah suka aikata na cin mutuncin manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam). Wanda hakan ya kai ga samun raddodi daga maluma na sunnah har da ma malaman Bid’ah wanda abin ya wuce tunaninsu. Kaman yanda ya gabata na gabatar muku da raddin malaman sunnah biyu Dr Sani Umar Rijiyar Lemo Da Kuma Sheikh Abdallah Gadon Kaya yau zan kawo muku raddin wani malamin Darika amma ta Qadiriyyah wato Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara. Shidai Abduljabbar Kaman yadda kowa ya sani ya shahara Da hayaniya Da Taratsi Da kuma kai harin Ta’addanci wa sahabban Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) da kuma magabata na kwarai irinsu bukhari muslim da sauransu. Shidai ba kafar baya bane wurin Ta’addanci acikin addinin musulunci, amma duk da wannan ta’addancin tasa ya ga cewa wa’innan ‘yan Tijjaniyya sunfishi har yaga ya dace Yayi musu raddi mai zafi. Masu sauraro sai kuyi hakuri Sabida acikin raddin tasa zakuga cewa yana kawo ayoyi da kurakurai kuma Ihu da taratsi tayi yawa awurin. Hakan ta samo nasaba ne kan abinda ya gine mabiyansa kan hayaniya da Ihu. Sannan kawo ayoyi da yakeyi da kurakurai ta samo asali ne kan rashin hadda da yake fama da ita kamar yadda shi ya fada da kansa acikin wasu karatuttukansa. Kada na cikaku da bayanai domin sauke wannan raddi DANNA NAN. Ayi sauraro lafiya wassalamu alaikum.

Advertisements

19 thoughts on “Raddin Abduljabbar dan Taratsi Ga Mulhidan ‘Yan Tijjaniyya

  1. ya Allah ka’azamu ayar nan ta ihdinal siradal mustaqim siradal lazina an amta alaihim gairul maglubi alaihim walallalin Amin, kahade kawunan mu Baku daya

    • Jabberiya ko shi a

      kai jabberi kazo kanata iho dan gidan karibu ya ci mutuncin ubanka, ashe ba budadi karkamanta da irin cin mutuncin dakakewa magabta na kwarai. Kaga ramuwace kenan. Dan nasan wallahi ma,awuyya yafi nasuru

  2. abdul jabbaru bai san komai ba sai lakca da hayaniya da yima manzon allah karya da karyata gaskiya da karyar ilimi wai har yana hada kanshi da sheikh jafar wajen ilimi amma har yanzu ya kasa sanyawa shkh alkasim rana su zauna saidai kullun karyar ilimi da kwarewa amm yana tsoron a zauna da shi ayi muqabala

  3. Bai kamata kuyi wannan 6atanci ga AbdulJabbar ba. Kuyi kira ga addinin Allah, ba amfani da kalaman da zasu rika kawo rabuwar kan Musulmai ba, musamman a wannan lokacin da ake da matukar bukatar hadin kan Musulmai.

  4. Bawan Allah Abdul Jabbar yafi karfin yadda kake sammani.Idan hujjah kakeso sai ka sameshi domin kuwa shi baya magana saiya kawo aya da hadisi ba irinna wasuba ba aya ba hadisi.domin shi kuwa duk inda wani yayi badaidaiba sai yagaya masa.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s