DARAJOJIN ANNABI SAW(.40 )(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)


1 SHINE SHUGABANNI YAN
ADAM BAKI DAYA
2 SHINE MAI TUTAR YABO
RANAR ALKIYAMA
3 SHINE WANDA TUN DAGA
ANNABI ADAM SAW, HAR ZUWA
KASA SUNA KARKASHIN TUTAR
SA RANAR KIYAMA.
4 SHINE FARKON MAI NEMAN
CETO


5 SHINE FARKON WANDA ZAA
BAWA CETO.
6 SHINE AKA YAFE MASA
ABINDA YA WUCE DA ABINDA
ZAIZO ( IDAN MA YAYI)
7 SHINE ALLAH YAYI RANTSUWA
DA RAYUWAR SA
8 SHINE WANDA ALLAH TAALA
BAYA KIRANSA DA SUNAN KAI
TSAYE, (SAW) , SAI YA ANNABI
YA MANZO YA MAI LULLUBA
9 SHINE WANDA YA JINKIRTA
ADDUAR SA CETO GA
AL’UMMAN SA RANAR
ALKIYAMA
10 SHINE WANDA DUTSE YAKE
YI MASA SALLAMA.
11 SHINE WANDA KUTUTTURAN
DABINO YAYI KUKA SABODA
RABUWA DA SHI.
12 SHINE WANDA RUWA YA
FITO TA TSAKANIN HANNUNSA.
13 SHINE WANDA AKA CIREWA
WANI SAHABI IDO A WAJAN
YAKI YA MAYAR MASA NAN
TAKE. KUMA YA WARKE NAN
TAKE .
14 SHINE WANDA YAFI KOWA
KYAWUN HALITTA
15 SHINE WANDA YA FADI
KOWA KYAWUN HALI
16 SHINE WANDA ZAA DOSA
RANAR ALKIYAMA, BAYA ANJE
WAJAN KO WANNE ANNABI, YA
BADA UZRI
17 SHINE AKA AIKO GA DUK
DUNIYA, AMMA SAURAN
ANNABAWA GA AL’UMMAR SU
KAWAI.
18 SHINE WANDA KASA ZATA
FARA TSAGEWA YA FITO RANAR
ALKIYAMA.
19 SHINE WANDA MAI WASEELA
DA FADEELA
20 SHINE MAI TAFKIN KAUSARA.
21 SHINE WANDA ZAI FARA
SHIGA ALJANNAH DA
AL’UMMAR SA.
22 SHINE WANDA MUTUM
DUBU 70 ZASU SHIGA
ALJANNAH BABU HISABI DAGA
AL’UMMAR SA.
23 SHINE LITTAFIN SA YAFI
DUKKAN LITTAFIN DA AKA
SAUKAR.
24 SHINE WANDA AKA
HALASTAWA AL’UMMAR SA
GANIMA BAYAN TA HARAMTA
GA WADANDA SUKA GABATA.
25 SHINE WANDA AKA
HALASTAWA AL’UMMAR SA SUYI
TAIMAMA DA KASA
26 SHINE WANDA AKA
SANYAWA AL’UMMAR SA KO’INA
YA ZAMA MASALLACI IN BANDA
MAQABARTA DA BANDAKI
27 SHINE WANDA AL’UMMAR SA
TAZO A KASHE, AMMA TAFI
WADANDA SUKA GABATA
DARAJA
28 SHINE WANDA YAYI ISRA’I DA
MI’IRAJI HAR SUKA YI MAGANA
DA ALLAH TAALA, HAR YA
KARBO SALLAH
29 SHINE WANDA YAFI
ANNABAWA YAWAN MABIYA DA
YAWAN LADA
30 SHINE WANDA AKA
NINKAWA AL’UMMAR SA AIKIN
LADA DAYA, ZUWA GOMA
31 SHINE MU’UJIZAR SA BATA
YANKEWA DA WUCEWARSA
32 SHINE WANDA DUK YA BISHI
ZAI SHIGA ALJANNAH WANDA
YA SABA MASA BAYA SO
33 SHINE WANDA IDAN KAYI
MASA SALATI DAYA, ALLAH ZAIYI
MAKA GOMA.
34 SHINE WANDA ALLAH YA
SANYA MAKULLAN TASKOKIN
KASA A HANNUNSA.
35 SHINE WANDA YAFI KOWA
SAN ALLAH, KUMA ALLAH YAFI
SON SA.
36 SHINE WANDA SAI KAFI SON
SA, FIYE DA IYAYANKA, DA
YA’YANKA, DA KANKA, DA DUK
DUNIYA BAKI DAYA.
37 SHINE WANDA IDAN KAYI
MASA SALLAMA, ALLAH YAKE
DAWO MASA DA RANSA YA
AMSA MAKA SALLAMAR KA.
38 SHINE WANDA AKA SIFFANTA
AL’UMMAR SA DA ADALCI DA
SHEDAR DA ZASU YIWA
ANNABAWA, AKAN SUN ISAR DA
SAKO.
39 SHINE WANDA AL’UMMAR SA
BATA HADUWA AKAN BATA.
40 SHINE SAHIBUL MAKAMIL
MAHMUD SAW.
ALLAH YA KARA MANA SON
ANNABI DA BIYAYYA A GARESHI.
ALLAH TSINEWA MASU TABA
DARAJAR ANNABI SAW.

Advertisements

5 thoughts on “DARAJOJIN ANNABI SAW(.40 )(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

  1. A dai kiyayi yi wa Allah ƙarya. Abin da ba a tabbatar daga Shi yake ba, kada ai zarɓaɓin gaya wa mutane. Irin wannan yahudawa suka yi Allah yai fushi da su. To yanzu gashi kuma kun ce kune gwanayen sanin sha’anonin Allah kuma masu shiriya – a biku a dace. To duk lomar da za ku gutsuro dai, ku tabbatar marar ta na Ƙur’ani.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s