Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka


Assalamu Alaikum ‘yan’uwa,  a takaice zamu dubi wasu hanyoyi na neman tsari daga sharruka ta duniya da lahira,  wanda addinin musulunci ya koyar damu.  kaman yanda kowa ya sani ne da yawa daga cikin mutane suna cikin tsoro, da rashin kwanciyar hankali, musamman a wannan zamani da fitintinu sukayi yawa, wasu mata zaka samu sukuma suna fama da matsaloli na bugun Aljannu. Duka wannan insha’Allah ana iya yin riga kafinsa Da yardar Allah,

Da farko abinda musulmi ya kamata ya gane shine komai ya sameshi daga Allah ne, babu mai iya cutar dashi ko amfanar dashi sai da yardar Allah, sabida haka in matsala ta sami musulmi abinda zai fara yi shine komawa zuwa ga Allah, kada yaje wurin boka, ko malamin tsubbu koma wace tarkace, domin ba abinda wannan zai iya masa.

Hanyoyin neman tsari:
1.Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace wa sahabinsa uqbah(Radiyallahu anhu)  kulhuwallahu, falaq, da nasi, babu wani abinda mutum zai nemi tsari dasu fiye da wannan. Musulmi ya kamata ya lazimci karanta wa’innan surori uku safe da yamma da kuma in zaiyi bacci.
2. Lazimtar yin Zikirori dabam dabam wanda annabi ya koyar,  zikirin kafin bacci,  da na tashiwa daga bacci, shiga bayan gida, fita daga bayan gida, shiga gida da fita dag gida..
Ya kamta mutum in ya fita daga gidansa ya karanta
أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق، اللهم إني أعوذ بك  أن أضل أو أضل،أو أزل أو أزل أو أظلم أو أظلم أو أجهل أو يجهل علي.
Sannan mutum ya karanta Kulhuwallahu da falaq da nasi kafa uku
Uku,  sannan In ya isa inda zai isa, yace
أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق.
Ma’ana: ina neman tsarin Allah daga sharrin duk abinda ya halitta.
Manzon Allah(sallallahu alaihi wasalam)  yace: “Duk wanda ya fadi haka babu wani abinda zai cutar dashi har yabar wurin, 
Sannan Yana daga cikin Hanyan kariya Bin dokokin Allah da kauce wa tsaba masa, Domin duk wanda yaji tsoron Allah yabi dokokinsa Allah zai kareshi kuma zai sashi yayi rayuwa mai kyau da nastuwa, 
Allah yace :
ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ ﺃﻭ ﺃﻧﺜﻰ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ ﻓﻠﻨﺤﻴﻴﻨﻪ ﺣﻴﺎﺓ ﻃﻴﺒﺔ ﻭﻟﻨﺠﺰﻳﻨﻬﻢ ﺃﺟﺮﻫﻢ ﺑﺄﺣﺴﻦ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻤلون.
Wanda yayi aiki na gari daga cikin maza ko mata yana mumini zamu rayar dashi rayuwa mai kyau kuma muyi masa sakamako da mafi kyawun abinda suke aikatawa.
Ayoyi masu irin wannan ma’ana suna da dimbin yawa a alQur’ani.  Ya zama tilas mutum maison sa’ada da tsira ranan tashin Qiyama ya rika kiyaye dokokin Allah ako wani lokaci iyakan iyawansa,
Sannan yawan karanta Alqur’ani shima yana bada kariya musamman karanta suratul baqara acikin gida,  yana kare Gidan daga sharruka dabam dabam, da shaidanu, kaman yanda Annabi(sallalahu alaihi wasallam) ya bada labari, 
Sannan mata masu fama da aljanu,  Yana da kyau su lazimci karatun AlQur’ani, da zikirin safe da yamma, sannan su guji barin gashin kansu a waje, da shiga marar kyau koda ko acikin gida ne, sannan inhar mace tana fama da aljanu yi mata aure yana taimakawa ta rabu dasu.

Allah yasa mudace, ya rabamu da duk wata musiba, duniya da lahira……


Click Here To Report any Error.

Advertisements

2 thoughts on “Hanyar Neman Tsari Daga Sharruka

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s