ISBALIN TUFAFI YANGA CE A MAHANGAR MUSULUNCI(Dr. Ibrahim Jalo)


Tabbas yin aiki da ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah cikin Aqidah, da Ibadah, da Mu’amalah shi ne alheri ga mutane duniyarsu da lahirarsu.
Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce Isbalin tufafi yanga ce. Imamu Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 4086 da isnadi sahihi daga Sahabi Jabir Bin Sulaim Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻭﺍﺭﻓﻊ ﺍﺯﺍﺭﻙ ﺍﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﺴﺎﻕ ﻓﺎﻥ ﺍﺑﻴﺖ ﻓﺎﻟﻰ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻭﺍﻳﺎﻙ ﻭﺍﺳﺒﺎﻝ ﺍﻻﺯﺍﺭ ﻓﺎﻧﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺨﻴﻠﺔ)).

Ma’ana: ((Ka dage zaninka zuwa tsakiyar kwabrinka, in ka ki to zuwa idon sawunka, ka nisanci isbalin tufa lalle shi daga yanga yake, kuma lalle Allah ba ya son yanga)). Babu Musulmin kirki da zai san wannan hadithi ingantacce sannan ya ci gaba da kiran mutane cewa su rika yin isbali matukar dai isbalin da suke yi ba saboda yanga ba ce suke yin sa! Saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya riga ya gama magana cewa zatin isbalin kansa yanga ce.
*********************
A nan akwai abubuwa guda biyu wadanda suka banbanta da juna, kuma Shari’a ta banbanta su cikin hukunci. Wanannan abubuwa biyu su ne kamar haka:-
1. Wanda tufarsa ta yi kasa da idon sawu koda kuwa ba ta ja kasa ba, shi wannan hukuncinsa shi ne cancantar shiga wuta.
Imamul Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 5450′ daga Sahabi Abu Huraira Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻣﺎ ﺍﺳﻔﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻌﺒﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻻﺯﺍﺭ ﻓﻔﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ )).
Ma’ana: ((Abin da ya yi kasa da idanun sawu daga tufafi to yana cikin Wuta)).
2. Wanda tufarsa ke jan kasa da niyyar yanga, shi wannan hukuncinsa shi ne Allah Madaukakin Sarki ba zai dube shi ba a Ranar Kiyama.
Imamul Bukhari ya ruwaito hdithi na 3465, da Imamu Muslim hadithi na 2085 daga Sahabi Abdullahi Bin Umar cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻣﻦ ﺟﺮ ﺛﻮﺑﻪ ﺧﻴﻼﺀ ﻟﻢ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻴﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ )).
Ma’ana: ((Wanda duk tufarsa ta ja kasa saboda yanga Allah ba zai dube shi ba a Ranar Kiyama)).
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tausaya mana Ya mana baiwar jin saukin riko da sunnar AnnabinSa mai taira da amincin Allah. Ameen.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s