Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuceshi


Mutum ne yazo sallan gawa sai ya tarar da liman ya riga yayi kabbara biyu ko fiye da haka meye hukuncinsa? zai yi kabbara ya fara daga karatun fatiha ne ko kuma zai fara daga  inda limamin yake ne sannan daga karshe ya rama kabbarorin ko kuma bazai rama su ba?

Amsa:

idan mutum wasu kabbarori suka wuceshi daga cikin kabbarorin sallan gawa toh in yazo zaiyi kabbara ne sannan ya fara karanta fatiha, zaiyi lura da cewa wannan kabbarar itace farkon kabbararsa, sannan in limami ya kammala sallan shikuma zai tsaya ya kammala kabbarorin da suka wuceshi da sauri, in har ba’a dauke gawar ba, amma in aka dauke gawar to kawai zaiyi kabbarorin da suka wuce masa ne ajere ba tare da bata lokaci ba ko yin
addu’oi bayansu, dalilin da yasa malamai sukace wanda wasu kabbarori suka wuceshi na sallan gawa zai cikesu shine umumin fadin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam),

“IDAN AKA TAYAR DA SALLAH KU TAFI ZUWA GARETA KUNA MASU NATSUWA, ABIN DA KUKA SAMU KU SALLATA, ABINDA YA KUBCE MUKU KUMA KU RAMA” wannan hadisi bai bambance tsakanin salloli ba, kuma shima sallan gawa sallah ne kaman ko wani sallah,

haka ibn Baaz ya bada fatwa.  majmu’ul fatawa 13/149.

an tambayi maluman lajnatudda’imah,
Meye hukuncin wanda ya riski kabbara daya da liman a sallan gawa, kabbarori uku suka wuceshi?
sai suka amsa da cewa “Zai cike sallan gawarsa sai yayi kabbarori ukun da ya kubce masa kafin a dauke gawar, sannan zaiyi lura da kabbarar farko da ya samu da liman shine farkon sallan sa.
Wanda kuma kabbarorin sallan idi suka wuceshi wasu malamai suna ga zai ramasu da zarar ya shiga sallah bayan kabbarar harama sai yayi su baki daya, wannan itace mazhabar malikiyyah da shafi’iyyah ta daa… kuma ita tafi kusa da daidai,

wasu kuma suna ga basai ya rama ba sabida sunnace wanda muhallinta ya riga ya wuce, Allahu A’alam.


Click Here To Report any Error.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s