Falalar Azumi Ranar AaShuraa


Waccece Ranar Aashuraa?

Ranar Ashura itace rana ta goma ta watar Almuharram A Kalandar musulunci,.

Meye Falalar Azumtar wannan Rana??

An rawaito hadisi daga manzon Allah(Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: “Azumin wannan rana yana kankare zunuban shekara da ta gabata” Muslim 1162.

Shin Wannan zunubai da ake kankarewa Duka Har da manyan zunubai ne?

Wannan zunubai da ake kankarewa Kananun zunubai ne kawai, kaman yadda da yawa daga cikin maluman Ahlussunnah suka tafi akai, shi babban laifi yana neman ayi Tuba tukunna.

Shin ya tabbata cewa a azumci rana ta tara kafin ta goma?

Eh, An rawaito Daga Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) Yin azumin ranar goma ta watan almuharran, sannan yayi niyyar yin azumin ranar tara saboda ya tsaba wa yahudawa domin ance masa Suna girmama wannan ranar,(Muslim 1916).

Shin ya tabbata A addinin musulunci mutane su taru ranar ashura suna kuka suna yanka jikkunansu Domin Nuna Bakin ciki?

Bai tabbata ba koda a hadisin karya, cewa manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) yana nuna bakin cikinsa a wannan rana, da yin kuka, haka nan ba’a rawaito daga sahabban manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) cewa sun kasance sunayin haka ba, hakanan tabi’ai ma da masu binsu ba’a samo daga garesu sunayin haka ba, wannan Aiki ne na ‘yan shi’ah, wanda suka kirkiro bashi da asali a addini, Abinda ya tabbata a Sunnar annabi shine muka ambata a sama, na cewa Azumi akeyi a wannan rana, duk maison koyi da annabi(sallallahu alaihi wasallam) sai yayi azumi a wannan rana.

Allah nuna mana gaskiya ya bamu ikon binta ya nuna mana karya ya bamu ikon kauce mata.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s