Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi’ah


Abune sananne cewa musulmai sun rarrabu kashi kashi, Wasu sun dauki tafarkin Annabi(Salllahu alaihi wasallam) abin binsu, wasu kuma sun dauki Tafarkin waninsa a matsayin tafarkin da suke bi, haka abin yake acikin lamura masu yawa na addini, daga ciki akwai wannan rana ta Ashura aciki, zamuyi bayani a takaice kan halin musulmi na kwarai acikin wannan rana, da kuma halin Masu tsaba wa Annabi(Sallallahu alaihi wasallam)

Halin ‘yan Addinin shi’ah a ranar Ashura: Su ‘yan shi’ah sun dauki wannan rana a matsayin rana ce ta bakin ciki domin itace ranar da aka kashe jikan manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) “Alhussein” sukan fita acikin wannan rana cikin bakaken kaya, Suna yanka jikkunansu suna kuka suna fadiwa a kasa, saboda nuna bakin ciki, kuma sun dauki wannan a matsayin Addini, Wanda Hakan bashi da tushe a addinin musulunci, Kuma hakan yana nuna jahilci karara ta yadda suke mancewa da cewa Ali(Radiyallahu anhu) shima Shahada yayi, amma sai suka barsa basu mishi irin wannan makoki, duk da cewa Ali(Radiyallahuanhu) yafi Hussein Daraja.

 ya zama wajibi ga musulmi na kwarai ya kaurace wa irin wa’innan Bid’oi

Halin Wasu Masu Bid’ah a wannan Rana: wasu kuma daga cikin masu bin tafarki gurbatacce sun mayar da wannan rana wata rana ce ta idi, Suke shirya bukukuwa iri iri, da girke girke na wuce gona da iri domin nuna farin cikinsu da sunan addini, wanda ba’a rawaito hakan daga manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) ba.

Halin Ahlussunnah acikin wannan rana: Ahlussunnah wal jama’ah acikin wannan rana suna yin azumi ne kaman yadda manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) ya umarta, basu wuce gona da iri, wa’innan sune Allah ya datar dasu zuwa ga tafarki madaidaici, muna rokon Allah(Subhanahu wata’ala) ya datar damu zuwa ga wannan hanya.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s