AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA’UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA II


Mai Rubutu:Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Date: October 30 2016


1. Lalle kafirta sayyidina Abubakar da sayyidina Umar da mafi yawan Sahabbai yana daga cikin manyan aqidun Shi’awa, hakan yana rubuce cikin lattattafansu na da, da na yanzu, suna kuma fadin shi da bakunansu a duk lokacin da suka sami damar hakan, babban malaminsu mai suna Muhammadul Khulainiy ya ruwaito cikin littafinsa Al-Kafiy 8/125 daga Musal Kaazim cewa an tambaye shi game da Abubakar da Umar, sai ya ce: ((Su kafurai ne, la’anar Allah da Mala’iku da Mutane gaba daya su tabbata a kansu. Wallahi babu wani abu na imani da ya shiga zuciyarsu, sun kasance wasu mayaudara ne, masu kokonto, munafukai ne har dai mala’ikun azaba suka dauki rayukansu zuwa bigiren kaskanci cikin gidan Zama)). Intaha.Har yau Khulainiy ya sake ruwaitowa cikin Raudah cikin littafin Kaafiy riwaya ta 341 daga Abu Ja’afar ya ce: ((Mutane sun kasance masu ridda bayan Annabi in banda mutum uku, sai na ce: wadanne ne ukun? Sai ya ce: Miqdad Bin Aswad, da Abu Zarr Al-Gifaariy, da Salmanul Faarisiy rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a gare su)). Intaha. Haka nan Zainud Dinin Nabaatiy ya ce cikin littafinsa mai suna As-Siraatul Mustaqeem Ila Mustahiqqit Taqdeem 3/921 ((Umar Bin Khattab ya kasance wani kafiri ne da yake boye kafirci ya kuma bayyana Musulunci)). Intaha. Haka nan Muhammad Nabiy Bin Ahmad At-Tuwaisirkaaniy ya ce cikin littafinsa mai suna La’aali’il Akhbari wal A’athar 4/29 ((Ka sani, mafi darajar gurare da lokuta da halaye, kuma wadanda suka fi dacewa a la’ance su a cikinsu -Allah Ya tsine musu- su ne a lokacin da ka kasance a inda ake fitsari sai ka ce a duk lokacin fitar najasa da kuma tsarki, ka rika maimaitawa a lokacin gama fitsarin: Ya Allah Ka la’anci Umar, sannan Abubakar da Umar, sannan Uthman, da Umar, sannan Mu’awiyah, da Umar, sannan Yazidu, da Umar, sannan Ibnu Sa’ad, da Umar. Ya Allah Ka la’anci A’isha, da Hafsah, da Hindu, da Ummul Hakam. Ka la’anci duk wanda ya yarda da ayyukansu har zuwa ranar Kiyama)). Intaha. Haka nan Ayatullahi Khumainiy ya ce cikin littafinsa mai suna Kash’ful Asrar shafi na 621 ((Lalle mu a nan ba mu da wata damuwa da mutanen nan biyu, da abin da suka yi ta yi na saba wa Alkur’ani, da yin wargi da hukunce-hukuncen Ubangiji, da abin da suke halattawa da haramtawa a bisa ra’ayin kansu, da abin da suka tsara na zalunci domin cutar da Fatimah diyar Annabi, da cutar da ‘ya’yansa, sai dai mu a nan za mu yi ishara ne zuwa ga jahilcinsu ga hukunce-hukuncen Allah da Addini)).

2. Wannan abu na cin mutunci da kuka ji ‘yan shi’ah ke yi wa Sahabbai kadan ne kawai muka dauko daga cikin manyan littattafansu, tabbas da za a ce dukkan zage-zagen da suka yi cikin lattattafan nasu za mu tattaro to da hakan zai kai mu ga rubuta wani littafi babba. Amma abin da masu hankali da adalci suka sani shi ne: Su ahlus Sunnah wal Jama’ah mutane ne da ke girmama dukkan sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Su mutane ne da ke barranta daga mummunar hanyar Shi’awa da Nasibawa gaba daya. Su mutane ne da ke kiyaye hakkin ahlul Baiti. Su mutane ne da ke yin magana har kullun a kan ka’idar ilmi da adalci. Su mutane ne da ke tabbatar wa duniya cewa: babu yadda za a yi Shi’awa -a dai shari’ance da hankalce- su tabbatar da musuluncin sayyidina Aliyyu tare da imaninsa matukar dai ba su tabbatar da musuluncin sayyidina Abubakar da Umar tare da imaninsu ba; babban Malami a duniyar ahlus Sunnah wal Jama’ah Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin littafinsa Minhaajus Sunnatin Nabawiyyah Fi Naqdi Kalamish Shii’atil Qadariyyah 2/58-65 ((Lalle dan shi’ah rafidhiy ba zai iya tabbatar da imanin Aliyyu da adalcinsa ba, ya kuma tabbatar da cewa shi dan Aljannah neba, ballanta ma Imamarsa, matukar dai bai tabbatar da hakan ba ga Abubakar, da Umar, da kuma Uthman; saboda a duk lokacin da zai yi nufin yin hakan ga Aliyyu shi kadai to hujjoji ba za su taimaka masa ba; kamar dai kiristan da yake son ya tabbatar da annabcin Almasihu ba tare da tabbatar da (annabcin) Muhammadu ba lalle wannan hujjoji ba za su taimaka masa ba. Idan Khawaarijawan da suke kafirta Aliyyu, ko Nasibaawan da suke fasikantar da shi suka ce: Lalle shi (Aliyyu) azzalumi ne mai neman duniya, ya nema wa kansa Khilafah, ya yi yaki da takwabi a kan hakan, ya kashe dubban Musulmi a kan hakan, har sai da ya kasa kadaituwa da hakan, magoya bayansa suka watse masa, suka hada kai suka yake shi; in har wannan magana magana ce ta banza da kariya, to kuwa lalle kasancewar maganar dan shi’ah rafidhiy game da Abubakar da Umar ita ce ta fi(cancantar) zama banza da kariya. In kuma abin da dan shi’ah rafidiy ya ce game da Abubakar da Umar yana da abin da zai kama hankali a cikinsa, to lalle abin da (banaasiben ya fada) shi ne zai fi kama hankali; domin abu ne sananne ga kowa da kowa cewa: mutumin da mutane suka shugabantar da shi a kan kansu a bisa zabinsu da yardansu ba tare da ya bugi kowa da takwabi ko da sanda ba, ba kuma tare da ya ba wa kowa kudi ba, suka kuma hada hankali a kansa, sannan bai ba wa koda mutum daya daga cikin danginsa na jini mukami ba, kuma bai bar wa magadansa wata dukiyar gwamnati ba, sannan a da ya mallaki dukiyar da ya ciyar da ita cikin tafarkin Allah bai kuma dauki maimakonta ba (a lokacin da ya zama khalifah), sannan ya yi wasiyyar cewa (in ya mutu) a maida dukkan wata dukiyar gwamnati da ke hannusa zuwa ga baitul mali (abin da ke hannun nasa kuwa) shi ne: wani tsohon mayafi, da wani saurayin rakumi, da wata kuyanga bakar fata, da makamcin haka, har ma Abdurrahman Bin Auf ya ce wa Umar: yanzu ka karbe wannan daga iyalan Abubakar? Sai ya ce: a’a Abubakar ba zai fidda hannayensa a kansu ba ni kuwa in zura hannayena a cikinsu ba. Ya kuma ce: Allah Ya yi maka rahama Abubakar- ka wahal da shugabanni bayanka. Sannan bugu da kari bai kashe wani musulmi saboda karfafa mulkinsa ba, bai kuma yaki wani musulmi da wani musulmi ba, a’a ya yi amfani da (su Musulmin ne) domin yakar wadanda suka yi ridda da kuma kafurai, har ma ya fara bude kasashe, ya kuma ayyana wani babban gwarzo a matsayin khalifansa; (gwarzon) da ya bude kasashe, ya tsara diwani, ya rayar da yin adalci da ihsani. Idan har zai halatta ga dan shi’a ya kira: irin wannan mutum (watau Abubakar) da cewa shi mai neman dukiya ne da shugabanci, to kuwa zai yiwu ga nasibiy ya ce: Aliyyu ya zan wani mutum ne azzalumi mai neman dukiya da shugabanci, wanda ya yi yaki saboda tabbatar da shugabancinsa har dai Musulmi suka yi ta kashe junansu, bai kuma yaki koda kafuri daya ba, babu abin da Musulmi suka samu a zamanin mulkinsa in banda sharri, da fitina cikin addininsu da duniyarsu. Idan kuma har ya halatta a ce: Shi fa Aliyyu dukkan abin da ya yi, to ya yi shi ne saboda Allah, amma dai an sami mush’kila ne daga sauran Sahabban da ke tare da shi. Ko kuma in ya halatta a ce: ai shi Aliyyu mujtahidi ne da ya dace da gaskiya, waninsa shi ne mai kuskure cikin wannan hali; to lalle zai fi zama halal a ce: Abubakar da Umar mutane ne da suka kasance masu yi saboda Allah, wadanda kuma suka dace da gaskiya cikin ijtihadinsu, illa dai kwai ‘yan shi’ah ne suka kasa fahimtar hakkinsu, suka zamanto masu yin kure cikin zarginsu; domin nisantar Abubakar da Umar daga shubuhar nema wa kai dukiya da mulki, ta fi nisantar Aliyyu daga shubuhar nema wa kai dukiya da mulki. Kuma shubuhar Khawaarijawan da suka zargi Aliyyu da Uthmanu suka kuma kafirta su ta fi kama hankali a kan shubuhar ‘yan shi’ah da suka zargi Abubakar, da Umar, da Uthman suka kuma kafirta su. In kuma haka al’amarin yake me kuke tsammani da halin Sahabbai, da Tabi’ai da suka ki yi ma (shi Aliyyu) mubaya’ah, suka kuma yake shi? Lalle su wadannan karfin shubuharsu ya zarce karfin shubuhar wadanda suke sukan Abubakar, da Umar, da Uthman; domin su (wadanda ke sukan Aliyyu) sun ce: ba za ta yiwu mu yi mubaya’a ga kowa ba sai ga wanda zai tsaida adalci a kanmu, ya kuma kare mu daga wadanda suka zalunce mu, ya karba mana hakkinmu daga wadanda suka zalunce mu, idan har ya kasa yin haka to kuwa lalle ya zan ko dai mai rauni ne shi ko kuwa azzalumi ne shi, yin mubaya’a ga mai rauni ko azzalumi kuwa ba zai zama wajibi a kanmu ba. In kuma har wannan magana maganar banza ce batacciya, to kuwa maganar mai cewa: Abubakar da Umar azzalumai ne, masu neman kudi da mulki ita ce ta fi cancantar zama batacciyar magana. Wannan al’amari babu mutum daya da ke da ilmi da basira da zai yi shakkar cewa haka yake. In kuwa haka ne, don Allah ta kaka za a kwatanta shubuhar Abul Musal Ash-Ariy wanda ya yi muwafaka da Amr (Bin Ass) a kan tube Aliyyu tare da Mu’awiya, da sanya al’amarin (mulki) ya zan abin shawara tsakanin Musulmai; ta kaka za a kwatanta wannan shubuhar da shubuhar Abdullahi Bin Sabaa da makamantansa wadanda suke ikirarin cewa (shi Aliyyu) Imami ne Ma’asumi? Ko shi abin bauta ne? Ko shi Annabi ne? Kai ta kaka ma za a kwatanta shubuhar wadanda suke ganin nada Mu’awiya khalifa, da shubuhar wadanda suke ikirarin cewa (Aliyyu) abin bauta ne, ko kuwa annabi ne? Lalle su masu irin wannan ikirari kafirai ne a bisa ittifakin dukkan Musulmi, sabanin wadancan (masu cewa Mu’awiya ya cancani zama khalifa). Sannan abin da zai kara fidda wannan al’amari a fili shi ne: su Shi’awa ba su isa su tabbatar da imanin Aliyyu da adalcinsa ba matukar dai suna kan wannan matafiya tasu ta shi’awa, ba su isa su tabbatar da (imaninsa da adalcinsa ba) sai in sun bi hanyar Ahlus Sunnah tukun; saboda idan Khawaarijawa da wasunsu cikin wadanda suke kafirta shi (Aliyu) ko suke fasikantar da shi suka ce: ba mu yarda da cewa shi (Aliyyu) mumini ba ne, a’a (mu a gurinmu) shi kafiri ne, ko azzalumi ne, kamar dai yadda su (Shi’awa) ke cewa game da Abubakar da Umar; to su Shi’awan babu wata hujja da za su yi amfani da ita domin tabbatar da imaninsa da adalcinsa, face ita wannan hujjar ta fi yin nuni a kan imanin Abubakar, da Umar, da Uthman. Idan su (Shi’awa) suka kafa hujja da tawaturin labarin musuluncinsa, da hijirarsa, da jihadinsa (shi Aliyyu) to lalle tabbas an samu tawaturin labari game da su ma wadannan (watau Abubakar, da Umar, da Uthman), kai ba ma su ba, a’a musuluncin Mu’awiya, da Yazidu, da sarakunan banu Umayyah, da banu Abbas, da kuma sallarsu, da azuminsu, da jihadinsu ga kafirai labarinsa ya tabbata ne ta hanyar tawaturi. In kuma (‘yan shi’a) suka yi ikirarin samuwar munafurci cikin daya daga cikin wadannan, shi ma bakharije (ko banasibe) zai iya yin irin wannan ikirarin. A kuma duk lokacin da su (Shi’awa) suka ambaci wata shubuha, to shi ma (bakharije, ko banasibe) zai iya ambatonshubuhar da tafi tasu girma. Idan su (Shi’awa) suka ambaci abin da tatattun makaryata ke cewa: wai Abubakar, da Umar da ma can munafukai ne a boye, makiya ne ga Annabi mai tsira da amincin Allah wadanda suka bata addininsa iya iyawarsu, shi ma bakharije (ko banasibe) yana iya fadar hakan game da Aliyyu, kuma ya kafa hujja a kan hakan ya ce: da ma (Aliyyu) yana yi wa dan baffansa hassada ne -domin da ma an fi samun adawa tsakanin ‘yanuwa na jini); saboda haka shi (Aliyyu) da ma can yana son ya bata addininsa ne to amma bai sami damar yin hakan ba a lokacin da shi (Annabi) da Khalifofin nan uku suke raye, har dai ya yi ta kokarin ya kashe khalifa na ukun, ya kuma kunna wutar fitina har dai ya sami damar kashe sahabban (Annabi) Muhammad, da al’ummarsa; saboda nuna kiyayya da adawa da shi, da ma kuma can ya kasance mai hada baki da munafukan da ke ikirarin cewa akwai allantaka da annabci tare da shi, duk da ya kasance yana bayyana sabanin abin da yake boyewa; saboda da ma can addininsa shi ne takiyyah, bayan ya kona su ne sai ya bayyanar da inkarinsa ga abin da suke fada, to amma a gaskiyan al’amari yana tare da su a boye; wannan shi ya sa ma masu addinin batiniyyah suke daga cikin mabiyansa, kuma sirrinsa na gurinsu, su kuma addininsu na badini daga gare shi ne yake. Watau shi bakharije (ko banasibe) sai ya fadi irin wannan magana da ake yadawa cikin mutane da yawa, fiye da yadda ake yada maganar Shi’ah Rafidha game da Khalifofin nan uku; saboda shubuhar Shi’ah ta fi rashin makama a kan shubuhar Khawaarijawa da Naasibawa, Khawaarijawa sun fi Shi’awa hankali da kyakkaywan nufi, su kuwa Shi’awa sun fi su yawan kariya da mummunan addini. Idan kuma (su Shi’awa) sun yi nufin tabbatar da imanin (shi Aliyyu) da kuma adalcinsa da nassin Alkur’ani a kan hakan, sai a ce da su: (lafazin) Alkur’ani A’am ne, girman yadda yake shafan shi (Aliyyu) bai zarce girman yadda yake shafan waninsa ba; saboda haka babu wata aya da su (‘yan shi’ah) za su yi ikirarin kebantuwarta da shi (Aliyyu) face sai an samu damar yin ikirarin kebantuwarta, ko kebantuwar kwatankwacinta, ko kebantuwar wacce ta fi ta da Abubakar, da Umar; saboda ita kofar ikirari ba tare da hujja ba babu wanda ba zai iya bude ta ba in ya so, sannan kuma lalle ikirarin falalar Shehunannan biyu (Abubakar, da Umar) karfin hujjarsa ya zarce ikirarin falalar waninsu. Idan kuma sun ce: hakan ya tabbata ne ta hanyar nakali da riwaya, (to sai a ce da su) nakali da riwaya game da wadancan (watau Abubakar, da Umar) shi ya fi yawa da sha’hara. Idan kuma suka yi ikirarin tawaturi, lalle tawaturin da ke can shi ne ya fi inganci. Idan kuma sun dogara ne da nakalin Sahabbai, to nakalinsu ga falalar Abubakar, da Umar shi ne ya fi yawa. Sannan kuma su (Shi’awa) sun ce Sahabbai sun yi ridda sai ‘yan kadan kawai, in kuma haka ne, to ta kaka za a karbi riwayar wadannan game da falalar wani mutum? Sannan kuma babu shi’ah cikin Sahabbai da za a samu nakalin tawaturi daga gare su; ke nan hanyar nakali yankakkiya ce ga barinsu matukar dai ba su bi hanyar Ahlus Sunnah ba, kamar dai yadda hanyar nakali domin tabbatar da annabcin Almasihu yake yankakke ga barin Kiristoci matukar dai ba su bi hanyar Musulmi ba; wannan kuwa kamar mutumin da yake son ya tabbatar da ilmin fikhun Bin Abbas ne amma kuma ba tare da ya tabbatar da ilmin fikhun Aliyyu ba, ko kuma (mutumin) da yake son ya tabbatar da ilmin fikhun Ibnu Umar ne amma kuma ba tare da ya tabbatar da ilmin fikhun mahaifinsa (Uamar) ba, ko kuma (mutumin) da yake son ya tabbatar da ilmin fikhun Alqamah, ko Al-Aswad ne amma kuma ba tare da ya tabbatar da ilmin fikhun Ibnu Mas’ud ba, ko makamcin haka daga cikin al’amuran da ake tabbatar musu da wani hukunci ba tare da an tabbatar da hukuncin ga al’amuran da suka fi su dacewa da hukuncin ba; lalle yin irin hakan tufka ce da warwarar da ba a yin ta a gaban wanda ke bin hanyar ilmi da adalci; saboda wannan ne za ga cewa Rafidawa suna daga cikin mutanen da suka fi kowa jahilci da bata, kamar yadda Kiristoci ke daga cikin mutanen da suka fi jahilci. Haka nan Rafidawa suna daga cikin mutanen da suka fi mutane mugun hali, kamar yadda Yahudawa ke daga cikin mutanen da suka fi mugun hali; ke nan a cikinsu (Shi’awa) akwai nau’in bata (da jahilci) irin na Kiristoci, akwai kuma nau’in mugun hali irin na Yahudawa)). Wannan shi ne karshen maganar Bujumim malamin Sunnah Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah Allah Ya kara masa yarda.

3. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya taimake mu Ya kara cusa soyayyar Abubakar, da Umar, da Uthman, da Ali, da sauran Sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah cikin zukatanmu. Ya taimake mu Ya kara cusa mana kiyayyar aqidun Shi’awa, da Khawarijawa, da Nasibawa ckin zukatanmu. Ameen.

Advertisements

One thought on “AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA’UN ALIYYU BIN ABI TALIB NE SHI KO KUWA WANINSA II

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s