FALALAR SALLAR ADDUHA


Assalamu Alaikum warahmatullah.

image

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ
ﺫﺭ رضي الله عنه  ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ :
” ﻳﺼﺒﺢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺳﻼﻣﻰ ﻣﻦ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺻﺪﻗﺔ، ﻓﻜﻞ
ﺗﺴﺒﻴﺤﺔ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﺤﻤﻴﺪﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻬﻠﻴﻠﺔ
ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻜﺒﻴﺮﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﺃﻣﺮ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ
ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻧﻬﻲ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻳﺠﺰﺉ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ
ﺭﻛﻌﺘﺎﻥ ﻳﺮﻛﻌﻬﻤﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺤﻰ

Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace ‘Kowani Gaba yana wayan gari da sadaka akansa.(Ma’ana wanda zai kaddamar)
Toh sai yaci gaba da cewa ‘Kowata tasbihi da mutum zaiyi sadaqa ce, ko wata tahmidi da mutum zaiyi sadaka ce. Ko wata tahlili da mutum zaiyi sadaqa ce. Kowace takbiri da mutum zaiyi sadaka ce. Umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna ma sadaka ce. Amma duka wa’innan ayyuka da aka lissafa, ‘Sallah raka’a biyu ta adduha ta isar wa mutum’ wato in mutum yayi wannnan raka’a biyu ta adduha ta isar masa ya sauke nauyin wannnan sadakokin dake kan gabobinsa.

Kaman yanda akace, mutum yana da gabobi tsakanin babba da karami guda 360 a jikinsa…

Sannan ita salatu dduha sunnah ce wanda akeso musulmi ya lazimceta. Domin falalarta kamar yadda tazo a hadisai da dama wanda wannan hadisin yana cikinta. A wani wuri annabi yace ‘Sallahce ta masu maida lamari ga Allah’ Ma’ana masu yawan tuba.

Sallar raka’a biyu ce zuwa takwas.
Ma’ana. In kayi raka’a biyu ta wadatar. In ka kara kuma ka samu karin lada. Lokacinta na farawa bayan bullowan rana kaman da minti 15 kuma tana fita kafin lokacin azahar da mintoci. Amma amfiso ayita a karshen lokaci ga wanda keda dama… Kaman yanda annabi yayi nuni da cewa ‘Lokacin da rana tayi zafi’ ai lokacinta.. Amma in mutum yayi kafin wannan lokaci yayi daidai…. Allah sa mudace.