Salatil Fatihi A Ma’aunin Musulunci (2)(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Wannan kenan, sannan a cikin
kokarin cewa Sayyidina Aliyyu shi
ne ya fara salatil fatihi akwai
karyata abin da shi wanda ya zo da
salatil fatihin ya fada na cewa an yi
masa wahayinta ne a takardar
haske, kamar yadda bayanin haka
ya zo a cikin littafin (Jawahirul
Ma’ani 1/58) shehu Tijjani ya ce,
“Ita salatil Fatihi ba Bakari ba ne ya
wallafata ba, a’a yadda abin yake,
shi Bakari ya fuskanci Allah ne
tsawon lokaci mai yawa a kan
Allah ya bashi wani salati ga
Annabi (S.A.W), wanda a cikinsa
akwai ladan dukkan salatai, da
sirrin dukkan salatai. Ya dade yana
neman wannan abu (a wajen
Allah), sannan sai Allah ya amsa
masa addu’arsa, sai Mala’ika ya zo
masa da wannan salati, a rubuce a
cikin takardar haske”.
Wannan shi ne asalin samun
wannan salati, kuma shi ne abin da
Mal Madu ya kamata ya kawo.
Wanda idan muka dubi wannan
magana da kyau zamu ga akwai
matsala mai girma wajen gasgata
wannan batu, saboda dai babu
wani mutum koma bayan Manzon
Allah (S.A.W) da zai ce Mala’ika ya
kawo masa wani abu, kuma a
karba a rika bautawa Allah da
wannan abu, bayan Manzon Allah
(S.A.W) har ya bar duniya bai
koyawa Al’ummarsa wannan abu
ba, yarda da wannan, tuhumar
Annabi ne (S.A.W) cikin isar da
sako, kuma yarda da ne da wani
Annabi ne bayan Manzon Allah
(S.A.W), wannan kuma shi ne sirrin
da ya sa wadanda basa yin ta, ba
sa bauta wa Allah da wannan
salati, ba kamar yadda Mal Madu
yake so ya nuna ba na cewa, ai
tunda lafuzzanta na da kyau ba laifi
a bautawa Allah da ita.
Wani Abin da Mal Madu ya kawar
da kansa daga gare shi, shi ne irin
dimbin ladaddakin da wanda ya yi
wannan salati zai samu a wurin
Allah, wanda shi ma wannan ba
daga Allah ba ne, ba daga Manzon
Allah (S.A.W) ba ne.
Mai karatu ga kadan daga cikin
ladan wanda ya yi salatil Fatiha
daga inda aka samo ta wato littafin
(Jawahirul Ma’ani 1/58 – 59)
Shehu Tijjani ya ce, “Salatil Fatihi
wani lamari ne na Allah, babu
mashigar hankula a cikinsa, da za
a kaddara cewa, a samu wata
al’umma dubu dari, a kowacce
al’umma akwai kabila dubu dari, a
kowacce kabila da mutum dubu
dari, kuma kowanne daga cikinsu
ya rayu shekara dubu dari, yana
yin salati dubu ga Annabi (S.A.W),
ba tare da ya yi salatil fatihi ba,
sannan a tara ladan wannan
al’umma gaba dayanta, a tsawon
wadannan shekaru gaba daya, da
ba za su kai ladan wanda ya yi
salatil fatihi sai daya ba” Tiskashi!!.
A wani wurin shehu Tijjani ya ce,
“Salatil fatihi sau daya ta yi daidai
da duk wani zikiri da tasbihi da duk
wani istigafari da duk wata addu’a
da aka yi a duniya, karama ce ko
babba sai dubu shida”.
A Wani wurin shehu ya nakalto
daga wanda aka saukar masa da
ita, wato Albakariy ya ce, “Wanda
ya yi salatil fatihi sau daya, kuma
bai shiga Aljannah ba, to ya kama
wanda ya zo da ita a wurin Allah ya
rike shi!”
Wannan kadan kenan fa, kuma
mafi saukin abin da aka fada ne,
na ladan wannan salatin, ban da
cewa tana daidai da Alkur’ani sai
dubu shida. To yanzu dan uwa mai
karatu, zai yiwu wanda ya san
wadannan abubuwa ya yarda da
wannan salati, har ya ce zai
bautawa Allah da shi, don kuwa,
duk wanda ya san wannan, ya
kuma ci gaba da bautawa Allah da
wannan salati, to ya yi imani kenan
wani mutum zai zo da wata ibada
bayan Annabi (S.A.W) da aka yi
masa wahayinta, kuma ta shafe
abin da Manzon Allah (S.A.W) ya
zo da shi wajen lada, kai har ta kai
mutum zuwa Aljannah!!. Tabbas
na san Mal Madu ya san hukuncin
yarda da cewa akwai wanda ake
masa wahayi bayan Annabi
(S.A.W). Allah ya kare mu.
A karshe ina so dan uwa Mal Madu
da ire-iren masu fahimtarsa, su
sani cewa, rashin yin salatil fatihi,
ko yarda da ita, baya nufin kafirta
duk wanda yake yinta ba ne
Saboda masu yin ta sun kasu gida
biyu ne :
1 – Kaso na farko : Wadanda basu
san hakikaninta ba, ba su san
yadda ta zo ba, ba su san abin da
aka dabaibayeta da su ba na lada,
da nuna fifikonta akan salatin da
Annabi (S.A.W) ya zo da shi, su dai
kurum an ce musu salati ne ga
Annabi (S.A.W), don haka suke
yinta. Wadannan babu abin da
suke bukata illa karantarwa da
nuna musu salatin Annabi (S.A.W)
na gaskiya, wanda ya zo da shi,
wannan kuma shi ne halin da yawa
daga cikin mutanen kasarmu.
2 – Kaso na biyu : Wadanda sun
san wadannan abubuwa, kuma
sun kudurce su, sun yarda da su,
don haka suka rungume ta suna yi,
to wannan hukuncinsu yana ga
Allah, amma dai alal hakika suna
kan hadarin barin musulunci,
saboda yarda da wahayin ibada ne
bayan Annabi (S.A.W).
Amma maganar wani ya ce yana
yin ta ne don salati ne, kuma bai
yarda da abin da aka fada na
falalarta ba, to wannan shi ma
dayan biyu ne :
1 – ko dai wanda yake yaudarar
kansa, ya san ba haka abin yake a
ransa ba, kurum dai ya fada ne,
don kada a ritsa shi da wadannan
abubuwa, ya kasa bada amsa.
2 – ko wanda bai san abin da aka
fada a kanta din ba, don haka yana
bukatar ya je ya kara binceke.
Allah Madaukakin Sarki ya datar
da mu, ya nuna gaskiya, ya bamu
ikon binta, ya nuna karya, ya bamu
ikon guje mata

Advertisements

38 thoughts on “Salatil Fatihi A Ma’aunin Musulunci (2)(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)

 1. to Mlm Rabe rijiyar lemo mizakace game d salatin malaman imam shafi i .dasukace wann salatin yafi kowane salati.allahumma salli alah sayyiduna muhammadu kullama zakahuzzakirina w gafala anzirihizzakirina km basu kebe kowane salatiba

 2. yan xu ne na tabbata wasu malaman ba sa karatu domin salatin FATI NA annabi be kuma duk me yin ta xai Shiga aljanna da izinin Allah

 3. Pingback: Salatil Fatihi A Ma’auninMusulunci (2)(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo) | sijangebii's Blog

 4. SUBHANALLAH! Ku masu Kare Salatil Fatih, har yanzu banji wani yace ga hujjar yin saba. Ba Wanda ya kawo Aya ko Hadisi ko wani bayani mai gamsarwa daga Sahabbai ko Tabi’ai akan ingancinsa ba.

 5. Haba saleem yazaka ce da salatil fatihi gwara tsumma wannan kuskure ne domin kuwa idan kaduba fassarar salatin zakaga cewa annabi aka dosa bawai son rai akayi ba

  • Haba saleem yazaka ce da salatil fatihi gwara tsumma wannan kuskure ne domin kuwa idan kaduba fassarar salatin zakaga cewa annabi aka dosa bawai son rai akayi ba

 6. Kai jahilci baiba….dama annabi yace wabda Allah ya nupeshi da alkairi sai ya fahimtar dashi addini. Menenne aibun salatil fatih??? Wahabiyawa bakwa karatu kuma baku fshimci addininba ….sabida kun wulaqanta manyan waliyai da sufaye wadanda sune suka tafiyar da sunnar annabi bayan wafatinsa da sahabbansa da tabiai…Allah ya ganar damu

 7. Malam, a koma makaranta da sawran karatu. Ga chawarata, ka samu daya daga cikin malaman tijjaniya ya baka karatu.

 8. Ni dai na dauki salatul fatih abisa salati wanda kowa ma zai iya hadawa matuqar kalmomin da aka hada basu kaucewa addini ba,Shi kuma salatin Ibrahimiyya na dauke shi abisa Salatin da in kai kana da lada biyu ladan sunnah da ladan salati sabanin sauran salatai wadanda su ladan salati ne kawai.

 9. Gaskia akwoi matsala, haba malam iliyasu yaza’a kawo sabon abu a musulinci kace bai shafe shi baccin kuma yana musulmi, ai inaga duk abunda ke cikin addinina ya shafeni saidai indama ita salatil fatin ba addininin bace, kuma da ka kawo misali da saiyaddina abubakar, ai bakace aiyar bata shafeshi ba,
  Kaikuma nasiru maganar ilimi akeyi ba zagi ba in kana dana ka sai ka kawo hujjah sai, a saurareka kaji
  Kaikuma gambarawa, ai ka mance Allah yace muyi ma Annabi SAW salati, sannan Annabi yace ga yadda zamuyi, watau kun kasa fahimtar yan izalah, ne,
  Dan izalah bai yadda cewa ba akwoi wani waliyyi wanda yakai Annabi SAW, shiyasa komi akace gashi yana da falala in ba Annabi SAW yafada bai yarda shiyasa akace kabar wanda shehu tijjani ya koyar ka dauki wanda bakin da baya karya ya kowar watau Annabi Muhammadu SAW

 10. yan izala baku fahimtar addini saboda aqidarku irin ta yahudawa cewa duk abinda kwakwalwa ta kasa ganowa ba gaskiya bane. ku sani ilmi irin na maarifa ba wai littafi zaka dauka ka ganoshi ba. ilmi ne wanda allah ke basuwa sakamakon tsalkakan zuciyya har ta sami wusuli saboda taqwa(wattaqullah wa yullimukumullah). masu wannan ilmi suke samun ainahin sirrin alqurani.misali inda ayar qurani take cewa”innallaha wa malaikatuhu yusalluna alannabiyyi ya ayyuhalladhina amanu sallu alaihi” sai allah ya sanarda shehu tijjani ta hanyar ilhama da ruuya ba wahayi sabo ba cewa salatil fatihi ta shigo cikin umumil aya da tayi umurni “sallu alaihi(kuyi salati ga annabi)”.salatul ibrahimiyya misali ne na wada ake yima annabi salati ba rufe kofar yin salati ga annabi aka yi ba don babu annabi yace kada ayi wani salati in ba wannan ba. wannan kashfi ya zo ma shehu tijjani haqiqatan. ko wahhabiyawa na son suce idan abu ya faru ga mutum shice abin bai faru ba? kuma cewa baannabe kawai malaika ke baiyana ma wata fahimta to da malaika ya baiyana ga maryam fa ?ita annabi ce .salatil fatihi ba sabo wahayi ba ne , fahimta ce ta maanar umarnin da ke ciki aya kamar wada mukayi bayani a sama.mutane irin su shehu usmanu danfodiyo sun sha baiyana wasu sirrori na quran ba tare da sun koya daga littafi ba. sai suce ilminda allah ya jefa zuciyarsu ba haka bane. abinda yassa wahabiyawa basu samun irin wannan ilmi zauqi(by experience)sabo da basu yawan ibada da zata tsalkaka zukatansu har ta sami annuri da zai sada ta da allah ta sami ilhama ko kashfi. suna kwantawa suna ta barci suna ta tusa bayan gama hawan mata.yaya zasu gano abinda wadanda”tataja junubihim anil madajii” zasu iya ganowa. ina fatar yan izala suna fahimtan abinda nake fada su daina hawan karan tsaye akan abinda basu san wada aka ganoshi ba. su sani taba mutuncin waliyyai irin su shehu tijjani nada hadari.shehu usmanu bin fodiyo ya fada cikin ihyaussunnatil muhammadiyya wa ihmadu bidiatu shaitaniyya a babin ihsan cewa inkarin karamomin waliyyai na kawo suul khatima(mugunyar mutuwa ba kalmar shahada) kuma an sha ganin yan izala na kuwwa lokacin daukan rai ba kalmar shahada sabanin yan dariqa. ku tambayi likitoci da mutane ke mutuwa gabansu

 11. Ni da inayin salatil fati amma tunda Nagano salatil fati jabun salatine na saki na tuba nakama original wato salatin Annabi da ya koyar da bakinsa mai tsaki

 12. Annabi ya ce; yana daga cikin kawun musuluncin mutum ya bar abinda bazai amfaneshiba. kuma ya ce ku tambayi ahalin abu idan kun kasance baku da ilimi game da abin

 13. Hakika maalaminku yayi bayani,Amman abin mamaki Kuma abin da yamanta shine;a duniyar muslunci Allahu S.W.T. da manzonsa Annabi Muhammad kuma shugaban halitta S.A.W. ne kadai zasu ce ABU kaza ya halitta ko kuma bai halitta ba. Amman abin haushi. kuma abin takaici yace maku salatul fatihi babu kyau Baku tambayarsa cewa shin Allah ne yace ba kyau ko manzon Allah koko a wane littafi yaga anfada bata da kyau .Inaba malaninku shawara cewa ya rage girman kai da tunanin cewa shi mai ilimi ne yatafi fadar malamai yasha namaki Yakuma Ji abunda malamai suka FADA akan salatul Fatihi.Kukuma yan kallo a koma makaranta wajen malamai na gaskiya acigagaba da karatu insha Allah zaa gane.

 14. Wawa, jahili, dakiki, dangin yahudu……banda jahilci da karancin ilimi, ai Sayyadi Ali (as) shine ya fara yin salatil fatih kuma yace yajine daga Annabi Muhammadu (saw)…kana nufin Annabi ne yayi karya ko sayyadi Ali, ko kuwa tsaban dakikanci ne da kiyayya da kuke yiwa Annabi wanda kungiyar Izala to koyar daku??? To wallahi kayi hattara in ba haka ba sai ka mutu da haushin kare kamar yadda sama’ila idris yayi ko kuma ka mutu babu kai a gangar jikinka kamar mahmoud gumi na kaduna

 15. Allahumma salli Ala sayyidina Muhammad Alfatihi lima ugliqa walkhatimi lima sabaqa nasirul haqqi bilhaqqi walhadi ila siradikal mustaqimi wa’ala ahlihi haqqa qadrhi wamiqidarihil azim.
  Muhammad Rabiu Rijiyan lemu babu shakka kana da ilimi ka kauda jahilci akanka amma sauran abu guda ne ka rasa,abunnan kuwa shine tsoma baki akan abunda bai shafeka ba yakamata ka kiyaye harshenka da abubuwa kamar haka dan iliminka ya amfane ka
  1.minal fahasha’i 2.walmunkar 3.wal kalamul kabihi 4.wa,aimanud dalaqi 5.wa,intiharul musulumi 6.wa,ihanatihi 7.wasabbihi 8.wattakawifihi .
  Amma ba,ad.
  Tambayana anan wai shin wasu lafuza ne abun ki ciki salatil fati? Ko kuna ganin akwai lafuxan da girmansu sun ma Annabi yawane cikin salatin?. AMMA kASAN SHEHU TIJJANI KUWA?IDAN BAKA SANSHI BA MENENÉ NAKA NASHIGA CIKIN LAMARINSA WANDA SHI BAI SHIGA CIKIN NAKABA? Kuma daka fada wasu daka cikin falalar salatil fati shin kaka ga wayanda sukai imani da ita basu karanta Alqur.anin ne? Koko basuyin sallarne?ko haddar Alqur.an?duk da ance karanta salatin sau daya yafi karanta Alqur,ani sau dubu shida?? Ko kana ganin cewa itace kadai salatin da sukeyi?. Sabila shehu ya sanardasu cewa idan akace ya ummurcesu dawani aiki toh su auwana ta da ma,aunin shari,a ta dace da maunin ko ta sabada ma,aunin, idan tayi daidai suyi inko ta saba to suyi watsi da ita maganar ba daga gareshi bane. sai yasa makaranta salatin haddan Alqur.ani suke tayi.
  MUSULUNCI YAZO MANA DA ADALCI SAI YASA AKA UMMARCEMU MUYI ADALCI. Rashin Adalci shi ya kawo mana rashin xaman lafiya akasarmu da duniya baki daya. Duk duniya babu abunda yakai Addini mahimmanci da xa,a baiyawa malamai masana addinin da mun xauna lafiya. Kaga idan da xaka lura likita bakowa ya iya ba tukin mota ko jirgi,mashin bakowa ya iyaba sai direbobinsu hakama gyaransu sai kanikancinsu haka alqalanci sai alqalai komai da komai da komai idan aka dorashi a hannun wa,yanda suka iya sai ka ga komai ya tafi daidai amma sai gashi abunda yafi komai mahimmanci kowa yace ya iya, mutum da ya haddace wani littafi wai shima ya xama shehu yana ba da fatawa ko tako ina harda inda bai karanta ba yana bada fatawansa .alhali ko karatun boko ne kowa da fanninsa kuma kowa xaifi xurfi ne akan fanninsa,idan ka tambayeshi akan wani fanni xaice maka bai saniba kuma dan yafada hakan baiyi abun kunya dan ba abunda yakaranta bane Kuma baka isa ka kirashi jahili ba. Malam inaso kasani Malamai masana addini sunce mana Antaba tambayan Sayyadina Abubakar ma’anar wata Aya cikin alqur’ani yace bai saniba alokacin kuma yana kalifanci sahabbai sukace ya kana kalifan manzon Allah(S.A.W) Atambayaka kace baka saniba sai yace masu to karya suke so yayi.toh kaga anan ashe ba gaxawa bane Atambayeka kace bakasani ba kuje ku tambaye masu yin abun Kamar yadda Allah Yace ‘Fas alu ahalazzikiri in kuntum laa ta’alamun”.
  TOH jama’a yakamata mui ma kanmu adalci kuma sai ai hattara kowa ya tsaya a inda Allah Ya ajeshi Dan azauna lafiya.

  • Soki burutso kenan@iliyasu ibn aliyu , kai amma ka iya bankaura. To wallahi bamu ba salatin karyan nan daku jinginashi da manzo. Allah sarki!!! Gaskia kasha gubar aqidar nan dawa. Amma allah yasa kagane cewa ba wani abu acikin aqidarku sai cuwa-cuwa, da kula kula, da kage kage da karerayi da sunan son manzo.

  • Soki burutso kenan@iliyasu ibn aliyu , kai amma ka iya bankaura. To wallahi bamu ba salatin karyan nan daku jinginashi da manzo. Allah sarki!!! Gaskia kasha gubar aqidar nan dawa. Amma allah yasa kagane cewa ba wani abu acikin aqidarku sai cuwa-cuwa, da kula kula, da kage kage da karerayi da sunan son manzo.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s