SHI’A DA KAFIRTA MUSULMI(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Duk mai bibiyar tattaunawar da ake yi
tsakanin ‘yan shi’a yan sha biyu da
yan uwa Ahlussunnah a fcbk zai ga
yadda yan shi’a suke yawan tuhumar
Ahlussunnah da cewa suna kafirta
musulmi, wani lokacinma ba a kan
wannan abu ake tattaunawar ba,
amma sai sun san yadda suka
lankwaso zance, suka karkatar da
hankulan mutane zuwa ga waccan
tuhuma ta karya, maras asali a cikin
littattafan Sunnah.
Amma abin da zai baka mamaki shi
ne a duk cikin kungiyoyin addini
babu kungiyar da ta kai shi’a kafirta
musulmi, tare da zagi da cin
mutuncin bayin Allah, wannan abu ne
da yake kunshe a cikin manya-
manyan littattafansu, ba wai tuhuma
ba ce ta karya maras asali irin wadda
suke wa Ahlussunnah, don haka ma
bari mu kawo kadan daga cikin irin
dimbin riwayoyinsu da suke tabbatar
da haka, watakila wasu daga cikinsu
wadanda aka rude su da karya da
takiyya su sake nazari, su fahimci
gaskiya.
1- Babban malaminsu Alkulainiy ya
kawo riwaya a cikin littafinsa mai
suna Alkafi 8/246 daga limaminsu
muhammad Al-bakir yana cewa,
“Mutane sun yi ridda bayan Annabi
s.a.w sai mutum uku, Almikdada dan
Aswad, da Salman Al-farisiy, da Abu
zarril Gifari”.
2 – hakanan dai ya zo a cikin Alkafi
1/233 Imaminsu Arrida yana cewa
“Babu wanda yake kan addinin
Musulunci wanda bamu ba kuma ba
dan shi’armu ba”.
3 – A wata riwayar a cikin Arrauda
Minal Kafi 8/2109) daga limaminsu
Abu Ja’afar yana cewa, “Ya kai Abu
Hamza wallahi dukkan mutane
gabadayansu yan zina ne banda yan
shi’armu”.
4- Babban Malaminsu Ni’imatullahi
Aljaza’iriy yana bayanin hukuncin
Nawasib – wato Ahlussunnah – ya ce
” Kafirai ne su, najasa ce da IJMA’IN
DUKKAN MALAMAN SHI’A
IMAMIYYAH, sun fi yahudu da nasara
sharri. Alamar Nasibi kuwa ita ce
gabatar da wanin Aliyyu a wajen
khalifanci”. Duba Al-anwarun
Nu’umaniyya 2/206 – 207).
Wannan kadan kenan daga cikin irin
riwayoyi da dimbin maganganun
malaman shi’a a kan kafirta duk
wanda ba dan shi’a ba, kuma wannan
ita ce akidar duk wani dan shi’a na
gaskiya, shi ne yana ganin kafircin
wanda duk ba shi’a ba ne, kai yana
ganinsa dan zina ne, kamar yadda
muke gani suna rubutawa a facebook
yayin tattaunawa da su.
A bangare guda kuma baza ka samu
irin wannan kafirtawar ba a litattafan
Sunnah, kai hatta shehun Musulunci
Ibnu Taimiyyah da Shehun musulunci
Muhammad Bin Abdulwahab
wadanda kullun ake tuhuma da yi
musu karya cewa su suka kawo
kafirta musulmi baza samu irin
wannan a cikin litattafansu ba, sai dai
a lankwasa musu magana ko a yi
mata mummunar fahimta. Allah ka
tsare da bata, ka dora mu akan
madaidaiciyar hanya.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s